Zaman zikira domin tunawa da Shekara daya da Waki'an Dan Uwa Musa Hassan Shinkafi da Sojoji




Naga Tashin Hankali da Shi ne Tashin Hankali na biyu dana gani a Rayuwata- Inji Musa Hassan Shinkafi

Nayi Matashin Kai Da kabari Har garin Allah ya Waye Batare Dana Sani ba-Inji Bello Abubakar AlPha

A Jiya Litinin 27, ga watan hudu ake cika Shekara Daya da Faruwar Waki'ar da Musa Hassan Shinkafi ya fuskanta tare da Bello Abubakar Alfa ta Zaluncin Da Sojoji sukayi musu a Garin Shinkafi.

Waki'ar ta Farune A ranar Assabar 27/04/2019, Da misalin karfe 7;00 na marece, Adaidai lokacin da ake Cikin tashe tashen hankalun Mahara a Zamfara. Wanda Ita kuma Waki'ar tafarune da Sojojin da aka turo a yankin Shinkafi domin Taimakon Al'ummar Wannan yanki na Shinkafi daga Hare-haren Mahara 6arayin Shanun.

Bayan Faruwar Abinda Yafaru tsakaninsa da Sojojin na Zalunci da Yimasa kwace da Sukayi, Wannan Waki'a bata Tsaya anan ba. Rayuwarsa tashiga cikin Hatsari da Rashin tabbas Wanda Kimanin Awa Ashirin da hudu Sojoji na Sintiri a gidansu Dan uwa Musa Hassan
 Wanda hakan yakai ga tilasta su yin Gudun Hijira Dashi da Dan uwa Bello Alfa, Daga Garin na Shinkafi Har Tsawon kwanakki da Watanni Batare da Suna Gidajensu ba, ko Ansan Inda Suke ba.

Bayan Dirar mikiyar Sojojin Sukayi Suka killace Unguwar
A Cikin Jawabin Musa Hassan Yake Cewa :- "Duk da yake ba Inason Insake kawo bayanin Abinda Yafaru bane tsakanina da Sojojin domin Bayanin ya rigaya ya gabata ga Al'umma, Inaso nayi Bayani akan Abubuwan da Sukafi daukar Hankalina acikin Wannan Waki'ar daga Farkonta har karshen ta.

Daga Cikin Abubuwan da Suka dauki Hankali na Shine Rashin Adalci da Shedar Zur da Wasu Ba'adin Yan uwa Suka Dora yadawa game da Wannan Matsalar Batare da Suna da labarin hakikanin Abinda ya faru ba.

Saboda Lokacin Da Waki'a din, tafaru Babu '
Wani Dan uwa da akayi agaban idon Shi, Babu Want Dan uwada ya nemi jin hakikanin gaskiyar Abin daga Garemu. Kuma Ni Ada Nasan Tarbiyyan da Su Syed Zakzaky (h), Suka Doramu akai Shine Fadar Gaskiya koda akan Abokin Hamayya ne. To Amma Sai gashi Mu bamusamu Wannan Adalcin ba Sam, na bincike na Gaskiya, da fadar Abinda ya faru koda ba'a bamu kariya ba, Matsayin mu na Yan uwa Ma'abota Addini.

DANNA NAN👇
☞ ͡Ahkham: Hukuncin  Masu Zama Da Janaba Da Gangan.. Futa Na Ɗaya (1)
☞ ͡Shekaru Sha Huɗu Masu Albarka
☞ ͡Nice Suhaila Ibraheem Zakzaky, Wa zai Tausaya Min??

Sannan kuma a lokacin Zuwan Jarabawa din Sai muka Rasa Yan uwantaka na Addini, Wanda Ita 'yan uwantaka na Addini a Tarbiyyan harka Shima Munsha Sawwala cewa Yafi na Yan uwantaka na jini. Sai Yazama Mun Rasa Yan uwantaka na Addini din kuma ma Har Yann uwan na Addini Suna bada Shaidar Zur Akanmu , Har Suna Kallon mu a matsayin Wadanda Bana Kirkiba Kuma Suna Dubinmu da wata manufa ta daban Wadda Baikamata su kallemu ba, Suna fadar Abunda Bamuyi ba, Kuma Basu gani ba, Kuma basuji daga Bakin muba a lokacin Faruwa Waki'ar, Suna Kallon mu Kamar ba 'Yan Harka ba, Alhali harkar ta Haifemu, acikinta muka taso kuma cikinta Mukayi wayo.

Hakika Idan Matsala ta taso ba akan taruwa azama daya ba, Lazim asamu Masu tunani da Hangen Nesa Wasu Ba'alin Yan uwa, Idan Sukaji Hankali ya kasa Daukar Abinda ake fada akan mu, Sai Su nemi Wata hanya ta neman hakikanjn gaskiyar Abinda ya faru damu. Kuma lalle Alhamdulillah Bayan Biyar Hanyoyin da yadace Suyi magana da Mahaifan mu, damu kan mu to Sunyi Abinda yadace Akanmu.. Allah (T) ya saka Masu da Mafificin Alkhairy....

Duk Dacewa Wannan Waki'a tafaru ne Abisa Zalunci da take hakki, Wanda A Ranar Bayan Bikin Abokina da kanena ne sojojin Suka taremu Suka Zaluncemu Inda nafito na Bayyana a Social Media, Cewa anzalunceni Kuma mutane Suka gani Kuma Suka Tausaya domin Sanin Cewa Anzalunce ni. Wannan ne Dalilin da Yasa Sojoji Suka dirar Mana Kusan kwana ukku 27-28-29 Allah ya kubutar Dani da Sauran 'Yan Uwan da muke tare.

Babban Abin da Yafi daukar Hankalina acikin Wannan Waki'a Shine Jajircewar Wasu Jajirtattun Ahaluss-Sunna Wanda ake tare dasu a zaman unguwa Wasu daga Cikin su, Suna Zaman Mutunci da Mahaifan mu ne, Wasu Kuma Muna Zaman Mutunci dasu ne, Wanda ta Wannan Dalilin ne Sukafito Suka Tara kawukansu Akan Wannan Matsalar Har Zuwa lokacin da ta kawo karshe. Gaskiyar Zance a Wannan lokacin Nafi Jindadi da Shauki ace Dan uwa daga Wajen gari idan Zai binciki hakikanin Abinda ya faru gareni to Idan da wata Hanya ya binciki Yan uwana najini, akan Matsalar ko mutanen gari Domin Sunfi Yi muna Adalci Sosai.

A karshe Dan uwa Musa Hassan, Ya kambala Jawabinsa da Darussa da Nasarorin da Ya samu akan Faruwar Wannan Jarabawa gareshi.

Kamar Yadda yake Ita Jarabawa ga Muminai Idan Suka maida Al'amarinsu ga Allah Sukan ga Alhairai bayan Wucewar ta.

To Nima Naga Darussa Sosai Daga ciki kuwa Akwai Wajabcin kara gyara Zamantakewa ta da Al'ummar gari Musamman Makwabtan mu, Abokani Sawa'un ko minene Fahimtar Su, domin Naga Natijar Zama da kowa lafiya a lokacin Faruwar Wannan Jarabawa.

Sai Abu Na biyu Jarabawar takaramin yakini akan Abinda Nakeyi na Gwagwarmayar Fada da Zalunci da Azzalumai koda akanwa Zalunci yake. Tunda yake Ni Almajiri ne ga Sheikh Ibrahim Zakzaky Kuma Nagani na tabbatar Duk Abinda Yasamu Malam (h), a kasar nan bai Sameshi ba Sai domin Fadar gaskiyarsa ga Azzaluman Mahukunta, da Fadansa da Zaluncin su ga Al'ummar kasar nan.

Kuma Alhamdulillah Nima Nayi Nasara. a Wannan lokacin kafin a zalunceni Ana cikin gayar Cin mutuncin Al'ummar gari, da keta Alfarmar mutanen gari, ga Abin ya damu Al'umma a gari Amma Ankj taymakonsu anzo Kuma anacin mutuncinsu Sunajin Tsoro basa iya Magana. Sai gashi Abin Yazo gare mu yan gwagwarmaya Kuma Dayake Azzalumai Mutane Suke Tsoro ba Allah ba. Daga Lokacin Muka fadi Halin da Al'hmma Suke ciki a Garin Shinkafi, Ba'a kara yiwa kowa ba Kuma da yawa Wasu suka Sami kafa Suma Suna ta Fadar Albarkacin bakin su a Social media.

Kaga Abin yayi Faida kuma yayi tasiri, Sako Kuma yakai Inda Akeso Alhamdulillah, koda tun a Ranar Sun kasheni da Jinina bai tafi a banza ba. Na tafi a matsayin Wani Dan Gwagwarmaya Wanda yake kyamar Zalunci.

Alhamdulillah Ina Kara Godiya ga Allah Wanda da Taimakonsa ne na samu Sabaty a Wannan Jarabawa Nasamu dakewa akan Fitintinun Yan uwa.

Alhamd Allah Cikin Ikonsa Allah ya taimakeni...

Daga karshe inayiwa Allah Godiya Sannan Ina Kara Godiya ga Babana Alhaji Hassan, gudumuwar Malamai na Irin Su Malam Ahmad Ibrahim, Dr. Aliyu Akilu Duk da Rashin kasncewarsa a Najeriya Shima ya kasa Samun Nutsuwa Sai Bayan Kawo karahen Jarabawar, da Jajirtattun Yan uwa marubutan mu na Harkar Musulunci da sukayi Abunda yadace Tare da 'Yan Uwa Ahaluss-Sunna da Sauran Takaitattun 'Yan uwa Dake Cikin Gari Allah ya saka maku Da mafificin Alkhairy...

A Jawabin Mlm Bello Abubakar Alfa Kuma Kamar Maganar Gudace Wadda tafi Addabarsu Tamaidasu Saniyar Ware da Masu Kallon Wasu Mutane da Baikamata ayimusu ba...

Daga karshe Aka watse taro da Alhinin Abunda Yafaru Ga Wadannan Bayin Allah , aka jajanta Masu Saboda Irin Zaluncin da aka masu suka Bayyana, kuma aka Zalunce su saboda Sunsa Alkalami sun bayyana WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post