Ko Kunsan Duk Wanda Yayi Sallah A Bayan Sahabi Umar Bashida Sallah ??_Inji Annabi (s) !!

 


ASHE ANNABI (S. A. W. W) BAI YARDA DA JAGORANCIN UMAR BN KHADDAB  BA  ???


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DUK WANDA YAYI SALLAH A BAYAN UMAR BA SHI DA SALLAH IN JI ANNABI (S. A. W. W) 


A daidai lokacin dana cikaro da wadannan riwayoyi sai da hankalina ya tashi sosai, domin ban taba tsammanin Annabi (S. A. W. W) zai fadi irin wannan magana game da Khalifah Umar Bn Khaddab ba.


Saninmu ne an sami riwayoyi da dama wadanda ke nuna matsayin Khalifa Umar har ma takai sau da yawa ayoyin na sauka saboda wani aiki nasa ko maganarsa, sai abin ya zama shari'a ga Annabi (S. A. W. W) da ma dukkan sauran muminai mabiyansa.


Amma cin karo da wadannan riwayoyi sun jefa ni cikin wani irin tunani wanda ban san maganinsa. 


Wadannan riwayoyi dai sunzo ne cikin SUNAN na  ABU DAWUD daya daga cikin manyan littafinmu na Ahlus-Sunnah. 


Ga riwayoyin nan kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇باب في اسْتِخْلاَفِ أَبِي بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:


BABI CIKIN KHALIFANTAR DA ABUBAKAR (R. A) 


4662- حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ مُحَمَّدٍ النُّفَيْلِيُّ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ سَلَمَةَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ إِسْحَاقَ قَالَ: حَدَّثَنِي الزُّهْرِيُّ حَدَّثَنِي عَبْدُ الْمَلِكِ بْنُ أَبِي بَكْرِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ الْحَارِثِ بْنِ هِشَامٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ زَمْعَةَ قَالَ لَمَّا اسْتُعِزَّ بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا عِنْدَهُ فِي نَفَرٍ مِنَ الْمُسْلِمِينَ دَعَاهُ بِلاَلٌ إِلَى الصَّلاَةِ فَقَالَ مُرُوا مَنْ يُصَلِّي لِلنَّاسِ. فَخَرَجَ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ زَمَعَةَ فَإِذَا عُمَرُ فِي النَّاسِ وَكَانَ أَبُو بَكْرٍ غَائِبًا فَقُلْتُ يَا عُمَرُ قُمْ فَصَلِّ بِالنَّاسِ فَتَقَدَّمَ فَكَبَّرَ فَلَمَّا سَمِعَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَوْتَهُ وَكَانَ عُمَرُ رَجُلاً مُجْهِرًا قَالَ: ((فَأَيْنَ أَبُو بَكْرٍ يَأْبَى اللَّهُ ذَلِكَ وَالْمُسْلِمُونَ يَأْبَى اللَّهُ ذَلِكَ وَالْمُسْلِمُونَ)). فَبَعَثَ إِلَى أَبِي بَكْرٍ فَجَاءَ بَعْدَ أَنْ صَلَّى عُمَرُ تِلْكَ الصَّلاَةَ فَصَلَّى بِالنَّاسِ. 


Abdullahi Bn Muhammad  Annufailiy ya bamu labari, Muhammad Bn Sulaiman ya bamu labari daga Muhammad Bn Ishaq yace: Zuhriy ya bamu labari, Abdul-Malik Bn Abubakar Bn Abdurrahman Bn Harith Bn Hishaam ya bamu labari daga babansa daga Abdullahi Bn Zam'ata yace; 


" Yayin da (jinya) ta tsananta ga Manzon Allah (S. A. W. W) ni kuma ina tare dashi cikin wasu jama'a daga musulmai sai Bilal ya kiraye Shi zuwa ga sallah. Sai yace; " KU UMARCI WANDA ZAI YIWA MUTANE SALLAH. "   Sai Abdullahi Bn Zam'ata ya fita, sai yaga Umar cikin mutanen, Abubakar kuma ba ya nan. Sai nace,  " Yaa Umar, ka tashi ka yiwa mutane sallah.  Sai ya wuce yayi kabbara. Yayin da Manzon Allah (S. A. W. W)  yaji sautinsa, da ma Umar ya kasance mutum mai bayyanar (da karatu ne yadda mutane daga nesa suna jin muryarsa), sai (Manzon Allah) yace; 


" INA ABUBAKAR YAKE ! ALLAH YA DA MUTANE SUNQI HAKA (basu yardar da sallar Umar ba),  ALLAH DA MUTANE SUNQI HAKA. "


Sai aka aika zuwa ga Abubakar, sai yazo bayan  har Umar ya riga yayi wannan sallah. Sai (Abubakar) ya yiwa mutane (sabuwar) sallah. "
4663- حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ صَالِحٍ حَدَّثَنَا ابْنُ أَبِي فُدَيْكٍ قَالَ: حَدَّثَنِي مُوسَى بْنُ يَعْقُوبَ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ إِسْحَاقَ عَنِ ابْنِ شِهَابٍ عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُتْبَةَ أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ زَمْعَةَ أَخْبَرَهُ بِهَذَا الْخَبَرِ قَالَ لَمَّا سَمِعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَوْتَ عُمَرَ قَالَ ابْنُ زَمَعَةَ خَرَجَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَتَّى أَطْلَعَ رَأْسَهُ مِنْ حُجْرَتِهِ ثُمَّ قَالَ: ((لاَ لاَ لاَ لِيُصَلِّ لِلنَّاسِ ابْنُ أَبِي قُحَافَةَ)). يَقُولُ ذَلِكَ مُغْضَبًا. 


Ahmad Bn Sahih ya bamu labari, Ibn Abiy Fudaik ya bamu labari yace; Musa Bn Ya'aqub ya bani labari Abdurrahman Bn Ishaq, daga Ibn Shihaab, daga Ubaidullahi Bn Abdullahi Utbabata, cewa Abdullahi Bn Zam'ata ya bashi labari irin wannan labari, yace; " Yayin da Annabi (S. A. W. W) yaji sautin Umar. Ibn Zam'ata yace,  sai Annabi (S. A. W. W) ya fita har ana ganin kansa daga cikin dakinsa, sa'an nan yace; 


" A'A !  A'A  !!  A'A  !!! IBN QUHAFATA NE ZAI YIWA MUTANE SALLAH (ba Umar ba)  !"


Yana fadar haka a fusace (inji Ibn Zam'ata) 


(SUNAN ABU DAWUD, BABUN ISTIKHLAFI ABUBAKAR, HADISI MAI LAMBA 4662-4663)


     ABINDA NAYI NAZARI 


Kamar yadda aka kawo cikin hadisi na farko cewa har Umar ya riga ya yiwa mutane sallah amma da Abubakar yazo sai da ya sake yiwa mutane sallah wannan na nuna cewa sallar da Umar ya ja bata karbu wajen Allah ba, domin ba a sake sallar data karbu. Idan kuwa har mutum zaiyi sallah a cewa wani ya sake ta ga mutane, to, shi wannan mai sallah na farko bai cancanta ace ya jagoranci mutane ba. Domin ko a yanzu aka ce don shugabanku ba ya nan sai wani babba daga cikinku ya jagorance sallah amma shugaban naku yace wannan sallah bata yiwu ba, to, lalle bai kamata ace wannan mutum ya qara yi muku jagoranci cikin wata sallah ba da dukkan sauran wasu harkoki na addini. 


Sannan kuma shi wannan mutumi ya zama abin zargi, kuma ma zai zama tamkar an tozarta shi ne cikin jama'a. 


A hadisi na biyu ma kusan wannan magana ce, sai dai kawai bisa furucin da ya fito daga bakin Manzon Allah (S. A. W. W) yana nuna cewa Allah ne bai yarda da sallar da Umar zai jagoranci mutane a kanta ba. 


Idan kuma aka ce wai don a nuna cewa Abubakar ne Khalifa, to, ai ko bai jagoranci wannan sallah ba zai iya zama Khalifa. In kuma fadin da ake yi ne cewa wai Annabi (S. A. W. W) yace ga Abubakar da Umar babu wanda zai jagorance su, to, sai nace ai cikin sallar da Umar din ya sallata babu Abubakar a cikinta ballantana ace Umar ya wuce gabansa. Sannan kuma ma ai wucewa gaban mutum ba shi ke nuna cewa ka fi shi ba, domin dukkan masu wucewa gaban mutane a sallah ba sunfi kowa bane daga cikin mabiyan nasu.


GASKIYA KUNA RIKITAMU CIKIN MAGANGANUNKU.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


      (08137925034)


18th May, 2021/ 7th Shawwal, 1442.

4 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

 1. Ya Allah ka tsinewa duk kafirin da ya kawo wannan kazafi kan manzon Allah, Sayyadi Umar Dan Khaddab yafi karfinku dukkan kafirai yan Shi'a

  ReplyDelete
 2. Ya za'a fassara hadisi, Kai Kuma ka yi zagi? Ai sai ka karyata fassarar, ko ka raunata hadisin, ko ka kawo hujjar da ta karyata abinda aka fada.
  Sai kawai ka yi zagi, kamar wani tababbe?

  ReplyDelete
 3. Wanda duk yayiwa Annabi SALLALLAHU ALAIHI WASALLIM karya to Dan wutane.Hankali bazai daukaba.Ku nemi jahilai kugayamusu.Amma mumunsan Allah ya yarda da Sayyidina UMAR Annabi ma ya yardashi.Dan Aljanna ne tun a duniiya.Saboda haka kuyi hakuri ya'yan sharri.

  ReplyDelete
Previous Post Next Post