Wata Sabuwa:- Sallar Da akeyi Yanzu Ba Irin Ta Annabi (S) Ba ce !! Inji..

SALLAR DA AKE YI YANZU BA IRIN TA ANNABI (S. A. W. W) BACE IN JI ANAS BN MALIK  !!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KADA KU ZARGI 'YAN SHI'AH DON SUN CE AN CANCANZA AL'AMRAN ADDINI 

Adalci shine mutum ya karbi gaskiya ko daga bakin wa ta fito, amma ba zai zama yiwa kai adalci ba ace komai gaskiyar maganar mutum matuqar ta saba fahinta ko abinda mutum ya sani yace ba daidai bane. 

Duk wanda ke karatu tare da nazari da kuma neman sanin gaskiya zai riqa cin karo da abubuwan da ake aikata su cikin muslimci da sunan ibada, amma kuma sunyi hannun riga da yadda Annabi (S. A. W. W) da Sahabbansa ke yi zamanin Manzon Allah (S. A. W. W). 

          MISALI 

Zakkah, 

Rabon gado da kuma Azumi. 

Taqaitawa nayi a matsayin babin misali, amma har sallah ma ba yadda Annabi (S. A. W. W)  ya koyar damu ake yi ba. 

Kada kuce 'yan Shi'ah ne kadai ke irin wannan magana , a'a ba haka bane, domin har manya daga cikin Sahabbai sun bayyana haka. 

Bari mu kawo misali da wani Sahabi duk kafa hujja.  Ka shi kamar haka; 

๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ

11757- ุญَุฏَّุซَู†َุง ุฒِูŠَุงุฏُ ุจْู†ُ ุงู„ุฑَّุจِูŠุนِ ุฃَุจُูˆ ุฎِุฏَุงุดٍ ุงู„ْูŠُุญْู…َุฏِูŠُّ , ู‚َุงู„َ : ุณَู…ِุนْุชُ ุฃَุจَุง ุนِู…ْุฑَุงู†َ ุงู„ْุฌَูˆْู†ِูŠَّ ، ูŠَู‚ُูˆู„ُ : ุณَู…ِุนْุชُ ุฃَู†َุณَ ุจْู†َ ู…َุงู„ِูƒٍ ، ูŠَู‚ُูˆู„ُ : " ู…َุง ุฃَุนْุฑِูُ ุดَูŠْุฆًุง ุงู„ْูŠَูˆْู…َ ู…ِู…َّุง ูƒُู†َّุง ุนَู„َูŠْู‡ِ ุนَู„َู‰ ุนَู‡ْุฏِ ุฑَุณُูˆู„ِ ุงู„ู„َّู‡ِ ุตَู„َّู‰ ุงู„ู„َّู‡ُ ุนَู„َูŠْู‡ِ ูˆَุณَู„َّู…َ ، ู‚َุงู„َ : ู‚ُู„ْู†َุง ู„َู‡ُ : ูَุฃَูŠْู†َ ุงู„ุตَّู„َุงุฉُ ؟ ، ู‚َุงู„َ : ุฃَูˆَู„َู…ْ ุชَุตْู†َุนُูˆุง ูِูŠ ุงู„ุตَّู„َุงุฉِ ู…َุง ู‚َุฏْ ุนَู„ِู…ْุชُู…ْ ؟ " .

              ۞۞۞۞۞۞

Ziyad Bn Rabi'i baban Khidashin Al-Yuhmadiy ya bamu labari yace, na ji baban Imrana Al-Jauniy yana cewa ;  Na ji Anas Bn Malik yana cewa, 
" BAN SAN WANI ABU A WANNAN ZAMANI WANDA AKE KANSA A ZAMANIN MANZON ALLAH (S. A. W. W)  ."


(Abu Imrana)  yace, sai muka ce masa;  " TO, INA SALLAH TAKE? " Yace, 

" YANZU (kun ga) ANA AIKATA WANI ABU  WANDA KUKA SANI CIKIN SALLAH ?"

    (MUSNAD-AHMAD) 


Sallar Annabi (S. A. W. W)  ya kasance yana yin basmala a farkon kowacce surah cikin sallolinsa, sannan kuma yana yin kabbarori bayan idar da sallah har sai wadanda ke waje ma sun ji sautin. 

Ya zo cikin Sahihul-Bukhari kamar haka, 

๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ

ุงู„ุฐูƒุฑ ุจุนุฏ ุงู„ุตู„ุงุฉ


-842- ุญุฏุซู†ุง ุฅุณุญู‚ ุจู† ู†ุตุฑ ู‚ุงู„: ุญุฏุซู†ุง ุนุจุฏ ุงู„ุฑุฒุงู‚ ู‚ุงู„: ุฃุฎุจุฑู†ุง ุงุจู† ุฌุฑูŠุฌ ู‚ุงู„: ุฃุฎุจุฑู†ูŠ ุนู…ุฑูˆ: ุฃู† ุฃุจุง ู…ุนุจุฏ، ู…ูˆู„ู‰ ุงุจู† ุนุจุงุณ، ุฃุฎุจุฑู‡: ุฃู† ุงุจู† ุนุจุงุณ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ู…ุง ุฃุฎุจุฑู‡: 
ุฃู† ุฑูุน ุงู„ุตูˆุช ุจุงู„ุฐูƒุฑ، ุญูŠู† ูŠู†ุตุฑู ุงู„ู†ุงุณ ู…ู† ุงู„ู…ูƒุชูˆุจุฉ، ูƒุงู† ุนู„ู‰ ุนู‡ุฏ ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…

Ishaq Bn Nasri ya bamu labari yace, Abdul-Razaq ya bamu labari yace, Ibn Juraij ya bamu labari yace, Amru ya bani labari daga baban Ma'abadin bawan Ibn Abbas yace, ya ba shi labari cewa Ibn Abbas ya ba shi labari cewa; 

" LALLE 'DAUKAKA SAUTI  NA AMBATON ALLAH YAYIN DA MUTANE SUKA JUYO DAGA SALLOLI NA WAJIBAI YA KASANCE A ZAMANIN MANZON ALLAH  (S. A. W. W) ."

Riwaya ta gaba kuma tana cewa, 

๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ
 
843-ูˆู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุจุงุณ: ูƒู†ุช ุฃุนู„ู… ุฅุฐุง ุฅู†ุตุฑููˆุง ุจุฐู„ูƒ ุฅุฐุง ุณู…ุนุช ูƒู†ุช ุฃุนุฑู ุงู†ู‚ุถุงุก ุตู„ุงุฉ ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุจุงู„ุชูƒุจูŠุฑ

Ibn Abbas (R. A) yace, 

" NA KASANCE INA SANI IDAN SUKA JUYO DAGA HAKA (yin zikiri) IDAN NAJI INA GANE CEWA ANNABI (S. A. W. W) YA IDAR DA SALLAH  TA HANYAR YIN KABBARORI 
"
 (SAHIHUL-BUKHARI, KITABUS-SALAT, BABUN ZIKR BA'ADA SALAT, HADISI MAI LAMBA 842-843)

           TAMBAYA 

Tsakani da Allah mutane 40% suna karanta basmala kafin karanta kowacce surah cikin sallolinsu  ? 

Ko kuma idan sun idar da sallah suna yin kabbarori  ?

Yanzu mutane ba shan ruwa suke yi kafin faruwar rana ba  ?

Ashe Imam Malik bai kawo mana cikin Muwaddah nasa cewa Umar Bn Khaddab da Usman Bn Affan sai sunyi sallar magriba suke shan ruwa  ba?

Ba Allah (T) ya hana yin azumi a halin tafiya ba  ? Har ma Annabi (S. A. W. W) yake cewa, 

" BA YA DAGA CIKIN AYYUKAN ALKHAIRI YIN AZUMI A HALIN TAFIYA ." Ba? 

ุญุฏุซู†ุง ุขุฏู…: ุญุฏุซู†ุง ุดุนุจุฉ: ุญุฏุซู†ุง ู…ุญู…ุฏ ุจู† ุนุจุฏ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฃู†ุตุงุฑูŠ ู‚ุงู„: ุณู…ุนุช ู…ุญู…ุฏ ุจู† ุนู…ุฑูˆ ุจู† ุงู„ุญุณู† ุจู† ุนู„ูŠ، ุนู† ุฌุงุจุฑ ุจู† ุนุจุฏ ุงู„ู„ู‡ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ู… ู‚ุงู„: 
ูƒุงู† ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ููŠ ุณูุฑ، ูุฑุฃู‰ ุฒุญุงู…ุง ูˆุฑุฌู„ุง ู‚ุฏ ุธู„ู„ ุนู„ูŠู‡، ูู‚ุงู„: (ู…ุง ู‡ุฐุง) .........

^ู„ูŠุณ ู…ู† ุงู„ุจุฑ ุงู„ุตูˆู… ููŠ ุงู„ุณูุฑ^

Bukhari yace, Adam ya bamu labari, Shu'ubatu ya bamu labari , Muhammad Bn Abdurrahman Al-Ansari ya bamu labari yace, na ji Muhammad Bn Amruu Bn Hassan Bn Aliyu ,daga Jabir Bn Abdullahi (R. A) yace; Manzon Allah (S. A.W.W) yana cikin wata tafiya sai yaga Zihaam da wani mutum sun shiga qarqashin wata bishiya (saboda zafin rana),  sai yace, 

" MWNENE WANNAN  ?"

Aka ce masa, " Mai Azumi ne  ." Sai yace; 

" AI BA YA DAGA CIKIN AIKIN ALKAHIRI YIN AZUMI A HALIN TAFIYA  ."

(BUKHARI, KITABUS-SIYAAM, BABUN LIMAN ZULLILA ALAIHI WASH-TADDAT HARRA, HADISI MAI LAMBA :1946)

Yanzu me mutane suke yi ? Kace min azuminsu suke yi cikin halin tafiya domin suna gudun ramuwa. Amma da shike sallar qasaru ba ramawa ake yi ba sai suna dabbaqawa. 

ALLAH YA QARA HASKAKA MANA SHIRIYA. 

#FREE SAYYID ZAKZAKY (H)  !

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍๐ŸผAdo Isah Guda.

        (08137925034)

5th March, 2021/ 22nd Rajab, 1442.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Ya kamata a sanya sunan wanda yayi maganar a cikin sharhin gundarin maganar

    ReplyDelete
Previous Post Next Post