Ahkham: Hukuncin Masu Zama Da Janaba Da Gangan






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AMSA DAGA FATAWAR SAYYID KHAMENE'I

TAMBAYA:- Idan mutum ya zauna cikin janaba (ba tare da yayi wanka ba)har aka kira sallar asuba, to, shin, ya halatta yayi azumi a wannan rana?

AMSA:- Babu wata matsala ga azuminsa in dai azumin nasa ba na Ramadana ko na ramakonsa bane. To, amma azumin Ramadana ko ramakonsa, idan har ba zai iya wanka ba, to, dole ne yayi taimama, idan kuma har ya bar taimama, to, azuminsa ba ya inganta.

LATSA NAN👇
☞ ͡Ahkam: Hukuncin Azumin Mace Mai Ciki, Ko Shayarwa
☞ ͡Shin, Har Yanzu Ba'a Sami Irin Waɗannan Malamai Bane??
☞ ͡Kaɗan Daga Cikin Nasihar Da Syed Khamene'i Yayi Wa Shugaba Buhari A 2015

TAMBAYA:- Idan yayi azumi na wasu adadin ranaku alhalin yana cikin janaba ba tare da ya san cewa tsarki daga janaba yana daga cikin sharadin azumi ba, to, shin, wajibi ne yayi kaffarar wadannan ranaku da yayi azumi a cikinsu da janaba, ko kuma ramakonsu kawai ya wadatar?

AMSA:- Idan mutum ya wayi gari da janaba alhali yana sane dacewa yana da janaba, to, amma ya jahilci wajibcin yin wanka ko taimama (kafin ketowar alfijir), to, wajibi ne a gare shi bisa Ihtiyadi yayi kaffara bayan ramako, sai dai idan jahilcin nasa ba a sakacinsa bane, to, anan ba wajibi bane yayi kaffara, kodayake ihtiyadi ne yin kaffara.

TIRQASHI, AIKI JAA KENAN !

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~28th April, 2020 KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post