Shekaru Sha Huɗu (14) Masu Albarka..!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ADADIN SHEKARUN ANNABI YUSUF (A.S)A KURKUKU

Tarihi shi ke maimaita kansa, kuma kuma sunnar Allah bata sauyawa, sannan abinda Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canza shi.

Manzannin Allah (A.S)basu taka matsayin da suka kai ba har sai da suka tsallake manya-manyan matakai masu tsaurin gaske.

ADADIN SHEKARUN SAYYID ZAKZAKY(H)KENAN A GIDAN KURKUKU

Annabi Yusuf (A.S)ya fada cikin wannan matsananciyar jarrabawa wacce har aka manta dashi tsahon shekaru 14 a kurkuku kafin Allah ya fitar da shi, kuma ya ba shi babban matsayi wanda matsayinsa ya qasqantar da dukkan wani matsayin masu matsayi, kuma ya fifita matsayin raunana.

KU KARÀNTA NAN👇
☞ ͡Banga laifin wanda yace zuwan Covid-19, nada alaƙa da abinda akai wa Zakzaky ba
☞ ͡Akwai wani lokaci zai zo al'umma zasu karkasu zuwa 73
☞ ͡Ahkham: Hukuncin masu zama da janaba da Gangan

Zuwa wannan lokaci da muke shike shine adadin shekaru 14 da Sayyid Zakzaky (H)yayi agidan kurkuku, domin kafin wannan mafi girman jarrabawar da ya fada, ya shafe shekaru 9 a gidan kurkuku a lokuta daban-dabam, yanzu kuma ya qara samun wasu shekaru 5, wanda idan aka hada su da 9 na baya ya cika adadin shekarun Annabi Yusuf (A.S)kenan a gidan yari (prison).

Ba bisa ganin dama ko son rai aka fitar da Yusuf (A.S)daga kurkuku ba sai don hango bala'in da suke fuskanta.

Saboda haka, da iznin Allah cikin adadin wadannan shekaru 14 Sayyid (H)zai fito cikin izza, azzalumai su qasqanta, raunana kuma su daukaka.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~28th April, 2020. KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post