ƘASAR YEMEN TA KADDAMAR DA WANI SABON HARI KAN KASAR TATSUNIYA,

 



-Bin Muhammad

2024-06-05 H.TV


Dakarun kasar Yemen sun sanar da kai hari kan birnin “Eilat” na haramtacciyar kasar Tatsuniya da wani sabon makami,


Dakarun kasar Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan yankin Umm al-Rashrash da ke haramtacciyar kasar Tatsuniya da makami mai linzami mai suna “Palastinu”, wanda rundunar sojin Yemen ta sanar a ranar Litinin.


Kakakin rundunar sojojin kasar ta Yemen Birgediya Janar Yahya Sare’e ya bayyana cewa: A ci gaba da taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta da kuma mayar da martani ga laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi kan ‘yan gudun hijira a birnin Rafah na Zirin Gaza, sojojin Yemen sun kaddamar da farmaki da makami mai linzami kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Tatsuniya a yankin Umm al-Rashrash da ke kudancin Falasdinu da aka mamaye. 


Kakakin Rundunar Sojin ta Yemen ya tabbatar da cewa: Sun samu nasarar cimma burin da suka sa a gaba, kuma dakarun kasar Yemen na ci gaba da gudanar da ayyukansu na soji domin nuna goyon baya da tallafawa al’ummar Falastinu.

Ustaz Sulaiman Bullet

Baban humaid Mnnu//Ng0027

@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post