Ƙasar Slovenia ta amince da kasar Falastinu mai cin gashin kanta a hukumance,

 



Slovenia ta zama kasa ta baya bayan nan a cikin Tarayyar Turai da ta amince da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a  hukumance.


A ranar Talata ne mafi yawan ‘yan majalisar dokokin Slovenia suka kada kuri’ar amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta, inda suka yi watsi da kiran zaben raba gardama da babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta yi kan hakan, da nufin kawo atrnaki kan wannan manufa.


A ranar 30 ga watan Mayu ne gwamnatin Slovenia karkashin jagorancin firaministan kasar Robert Golob ta sanar da matakin amincewa da kasar Falasdinu mai ci gashin kanta, wanda ya yi daidai da matakin da kasashen Spain, Ireland da Norway suka dauka.


Bayan sanar da amincewar a hukuamnce, gwamnatin Sloveniya ta kafa tutar Falasdinu tare da ta Slovenia da EU a wajen harabar majalisar ministocin kasar.


Wannan ya zo ne jim kadan bayan Firayim Ministan Norway Jonas Gahr Store ya tabbatar, a cikin wata kasida da jaridar Politico ta buga, cewa Norway ta amince da kasar Falasdinu a matsayin “tabbatacciyar kasa mai ‘yancin cin gashin kanta.”

@-Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post