SAYYIDAH FADIMAH AZ-ZAHRA(AS) ITA KADAI CE MACE A 'YA'YAN ANNABI MUHAMMAD(SAW) WACCE TA AMSA KALMAR "BANATIKA" (َبَناتِكَ) SAYYIDAH FADIMAH AZ-ZAHRA(AS) ITA KADAI CE MACE A 'YA'YAN ANNABI MUHAMMAD(SAW) WACCE TA AMSA KALMAR "BANATIKA" (َبَناتِكَ) ('YA'YAN KA) A AYAR يا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِأَزواجِكَ وَبَناتِكَ (Q : 33 : 59), KAMAR YANDA TA AMSA KALMAR "NISA'ANA" (MATANMU) A AYAR MUBAHALAH (ALI-IMRAN : 61):


Ahlus-sunnah kan ce:


Idan Sayyidah Fatimah(as) ce kadai mace a 'ya'yan Annabi Muhammad(saw); me ya sa Allah zai ce:


يا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِأَزواجِكَ وَبَناتِكَ...


"Ya kai Annabi! Ka ce wa matan aurenka da 'yayanka mata...".


(Quran : 33 : 59).


Amsa:


Sayyidah Fatimah(as) ita kadaice macen da ta amsa kalmar "BANATIKA" ('ya'yan ka); kamar yanda ta amsa kalmar "NISA'ANA" (matanmu) a Ayar Mubahalah:


ﻓَﻤَﻦْ ﺣَﺎﺟَّﻚَ ﻓِﻴﻪِ ﻣِﻦ ﺑَﻌْﺪِ ﻣَﺎ ﺟَﺎﺀَﻙَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻌِﻠْﻢِ ﻓَﻘُﻞْ ﺗَﻌَﺎﻟَﻮْﺍ ﻧَﺪْﻉُ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀَﻧَﺎ ﻭَﺃَﺑْﻨَﺎﺀَﻛُﻢْ ﻭَﻧِﺴَﺎﺀَﻧَﺎ ﻭَﻧِﺴَﺎﺀَﻛُﻢْ ﻭَﺃَﻧﻔُﺴَﻨَﺎ ﻭَﺃَﻧﻔُﺴَﻜُﻢْ ﺛُﻢَّ ﻧَﺒْﺘَﻬِﻞْ ﻓَﻨَﺠْﻌَﻞ ﻟَّﻌْﻨَﺖَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻜَﺎﺫِﺑِﻴﻦ


"Ka ce, ku zo, mu kira 'ya'yayenmu da 'ya'yayenku, da matayenmu da matayenku, da MU KANMU da ku Kanku, sai mu yi tsinuwa, mu roki La'antar Allah akan Makaryata."


(ALI-IMRAN : 61).


Dukkan Littattafan Tarihi, Tafsiri, Hadisi... sun riwaito Annabi(saw) ya fita da Hasan(as) da Husaini(as) ne; a madadin 'ya'yan Muminai kacokaf.


Kuma ya tafi da Sayyida Fatima(as); a madadin matan Muminai kacokaf (alhali yana da matansa fa!), Sannan kuma "Wa anfusana..." Sai Annabi(saw) ya fito Da Imam Ali(as) da Shi Annabin a matsayin Ali(as) shine "Nafsur Rasul".


A wannan ayar Mubahala Sayyidah FADIMAH(as) Ita Kadaice Macen Da Ta amsa kalmar  "NISA'ANA" (Matayenmu) Saboda haka "BANATIKA" FADIMAH(AS) Ce, Kamar Yanda A Mubahala FADIMAH(AS) Ita Kadai ce ta hau Mukamin "NISA'ANA", Kuma Sunanta Na KAUSAR Ya Dada Fito Da Mukaminta Na daya Tamkar Da Biliyon!


Malaman da suka riwaito wannan ayar ta sauka ne akan wadannan tsarkaka biyar din, daga bangaren Ahlus-Sunnah akwai:


• Imamu Muslim a Sahihinsa, J/4, sh/1873.


• Imamu Nasa'I a cikin Kasa'is, shafi na 89.


• Malam Tirmizi a Sunan dinsa, J/4, Sh/293.


• Ahmad bin Hambali a Musnad, J61, sh/175 (bugun Masar).


• Malam Hakim a Mustadrak, J-3, Sh/150.

Da sauransu Masu yawan gaske.


Ga nassin hadisin:


حَدَّثَنَا  قُتَيْبَةُ، قَالَ: حَدَّثَنَا  حَاتِمُ بْنُ إِسْمَاعِيلَ، عَنْ  بُكَيْرِ بْنِ مِسْمَارٍ، عَنْ عَامِرِ بْنِ سَعْدِ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ، عَنْ  أَبِيهِ  قَالَ:  لَمَّا أَنْزَلَ اللَّهُ هَذِهِ الْآيَةَ : (تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَكُمْ) الْآيَةَ، دَعَا رَسُولُ اللَّهِ(ص) عَلِيًّا وَفَاطِمَةَ وَحَسَنًا وَحُسَيْنًا، فَقَالَ : "اللَّهُمَّ هَؤُلَاءِ أَهْلِي".


- حكم الحديث: صحيح الإسناد


- صحيح مسلم ( 2404 ).


- سنن الترمذي  أبواب تفسير القرآن عن رسول الله(ص)  | باب : ومن سورة آل عمران ( 3724، 2999).


- مسند أحمد ( 1608 ).


A LARABCI KALMAR JAM'I (PLURAL) TAKAN ZO DA MA'ANAR MUFRADI (SINGULAR) DON GIRMAMA, MISALI, KALMAR نحن (MU) DA TA ZO A FADIN ALLAH:


إِنّا نَحنُ نَزَّلنَا الذِّكرَ وَإِنّا لَهُ لَحافِظونَ


"TABBAS, MU NE MUKA SAUKAR DA QUR'ANI, TABBAS MU ZAMU KARESHI".


(QURAN : 15 : 9).


Allahumma salli ala Muhammad wa'ali Muhammad!!!


Sani Muh'd Sani Muh'd 

Baban humaid Mnnu//Ng0027

@ma'asumah Nigerian News update


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post