SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS) CE KADAI 'YAR ANNABI MUHAMMAD(SAW) MACE, KUMA ITA KADAI CE MACE A 'YA'YAN SAYYIDAH KHADIJAH(AS):

 



Wasu masana tarihi sun tabbatar da cewa Annabi(saw) da Sayyidah Khadijah(as) basu da wata 'ya mace banda Az-Zahra(as). Sauran 'ya'yan Annabi(saw) da Sayyidah Khadijah(as) duk Maza ne (Al-Kasim da Abdullah; wanda akewa lakabi da Dayyib ko Dahir), Az-Zahra(as) kadai ce mace, kuma dukkan 'ya'yan Annabi(saw) sun sunyi wafati tun suna yara kanana, tun kafin a haifi Az-Zahra(as) in banda Ibrahim dan Mariya Al-Kibdiyya, shima ya rasu tun yana yaro karami.


Wannan dalilin ne yasa masana Ulumul-Qur'ani suke cewa an saukar Suratul-Kausar ne sabida gorin da kafirai ke yiwa Annabi(saw)


na mutuwar 'ya'yansa da rashin magaji, sai Allah ya bashi Az-Zahra(as), wannan yasa masana suka ce; Az-Zahra(as) ita ce Kausar. 


A 'ya'yan Annabi(saw) da Khadijah(as), Az-Zahra(as) ce kadai ta rayu, ta girma, tayi aure, ta haihu, har Imaman Ahlul-bayt(as) da sharifai  suka kasance ta tsatsonta.


ﻳﺆﻛﺪ ﺫﻟﻚ ﻣﺎ ﺫﻛﺮ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺑﻲ ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ﻭﺍﻟﺒﺪﻉ : ‏ﺃﻥ ﺭﻗﻴﺔ ﻭﺯﻳﻨﺐ ﻛﺎﻧﺘﺎ ﺍﺑﻨﺘﻲ ﻫﺎﻟﺔ ﺃﺧﺖ ﺧﺪﻳﺠﺔ.


Abinda yake tabbatar da cewa Sayyidah Khadijah(as) bata da wata 'ya banda Az-Zahra(as) shine abinda yazo littafin ﺍﻷﻧﻮﺍﺭ ﻭﺍﻟﺒﺪﻉ cewa:


"RUKAYYA da ZAINAB 'ya'yan Hala ne 'yar uwar Sayyidah Khadijah(as)".


ﻣﻨﺎﻗﺐ ﺁﻝ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﺝ 1 ﺹ 159 ، ﻭﺍﻟﺒﺤﺎﺭ ، ﻭﺭﺟﺎﻝ ﺍﻟﻤﺎﻣﻘﺎﻧﻲ ، ﻭﻗﺎﻣﻮﺱ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻛﻠﻬﻢ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﺎﻗﺐ.


Binciken masana tarihi ya kara tabbatar da cewa; itama Hala ('yar uwar Sayyidah Khadijah(as), RUKAYYA da ZAINAB din ba ita ta haifesu ba, 'ya'yan kishiyar ta ne. Ga nassin abinda ya zo a littafan tarihi masu yawan gaske:


ﻟﻘﺪ ﺭﻭﻱ ﺃﻧّﻪ ﻛﺎﻧﺖ ﻟﺨﺪﻳﺠﺔ ﺃﺧﺖ ﺍﺳﻤﻬﺎ ﻫﺎﻟﺔ، ﺗﺰﻭﺟﻬﺎ ﺭﺟﻞ ﻣﺨﺰﻭﻣﻲ، ﻓﻮﻟﺪﺕ ﻟﻪ ﺑﻨﺘﺎً ﺍﺳﻤﻬﺎ ﻫﺎﻟﺔ، ﺛﻢ ﺧﻠﻒ ﻋﻠﻴﻬﺎ - ﺃﻱ ﻋﻠﻰ ﻫﺎﻟﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ - ﺭﺟﻞ ﺗﻤﻴﻤﻲ ﻳﻘﺎﻝ ﻟﻪ : ﺃﺑﻮ ﻫﻨﺪ، ﻓﺄﻭﻟﺪﻫﺎ ﻭﻟﺪﺍ ﺍﺳﻤﻪ ﻫﻨﺪ . ﻭﻛﺎﻥ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﺘﻤﻴﻤﻲ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺃﺧﺮﻯ ﻗﺪ ﻭﻟﺪﺕ ﻟﻪ ﺯﻳﻨﺐ ﻭﺭﻗﻴﺔ، ﻓﻤﺎﺗﺖ، ﻭﻣﺎﺕ ﺍﻟﺘﻤﻴﻤﻲ، ﻓﻠﺤﻖ ﻭﻟﺪﻩ ﻫﻨﺪ ﺑﻘﻮﻣﻪ، ﻭﺑﻘﻴﺖ ﻫﺎﻟﺔ ﺃﺧﺖ ﺧﺪﻳﺠﺔ ﻭﺍﻟﻄﻔﻠﺘﺎﻥ ﺍﻟﻠﺘﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻤﻴﻤﻲ ﻭﺯﻭﺟﺘﻪ ﺍﻷﺧﺮﻯ؟ ﻓﻀﻤﺘﻬﻢ ﺧﺪﻳﺠﺔ ﺇﻟﻴﻬﺎ، ﻭﺑﻌﺪ ﺃﻥ ﺗﺰﻭﺟﺖ ﺑﺎﻟﺮﺳﻮﻝ ﻣﺎﺗﺖ ﻫﺎﻟﺔ، ﻓﺒﻘﻴﺖ ﺍﻟﻄﻔﻠﺘﺎﻥ ﻓﻲ ﺣﺠﺮ ﺧﺪﻳﺠﺔ ﻭﺍﻟﺮﺳﻮﻝ . ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻟﻌﺮﺏ ﻳﺰﻋﻤﻮﻥ : ﺃﻥ ﺍﻟﺮﺑﻴﺒﺔ ﺑﻨﺖ، ﻭﻷﺟﻞ ﺫﻟﻚ ﻧﺴﺒﺘﺎ ﺇﻟﻴﻪ ، ﻣﻊ ﺃﻧﻬﻤﺎ ﺍﺑﻨﺘﺎ ﺃﺑﻲ ﻫﻨﺪ ﺯﻭﺝ ﺃﺧﺖ ﺧﺪﻳﺠﺔ‏(ع‏).


An ruwaito cewa; Sayyidah Khadijah(as) tana da wata 'yar uwa mai suna Hala, ita Hala ta auri wani dan Kabilar Tamim mai suna Abu Hindu, Hala ce ta haifa masa wannan 'yar da ake masa alkunya da ita, mijin Hala ya auri wata matar daban (kishiyar Hala) ta haifi 'ya'ya mata 2, ana kiranasu; RUKAYYA da ZAINAB, mijin Hala da kishiyarta sun rasu, sai Hala ta rike 'yarta Hindu da 'ya'yan kishiyarta; RUKAYYA da ZAINAB (sabida ba wanda zai rike su), Sayyidah Khadijah(as) ta dawo da 'yar uwarta Hala a gidanta da zama, bayan Sayyidah Khadijah(as) ta auri Annabi(saw) sai Hala ta rasu, ta barwa Sayyidah Khadijah(as) 'ya'yan kishiyar ta; RUKAYYA da ZAINAB, sun taso a gidan Annabi(saw) kuma Annabi(saw) ya rikesu (har ya aurawa Usman dan Affan da su; daya bayan daya), (wasu masana tarihi, wadanda basu san yanda abin yake ba, ko kuma dalilai na murguda tarihi saboda siyasa) sai suka dauka cewa RUKAYYA da ZAINAB 'ya'yan Annabi(saw) ne, alhali 'ya'yan kishiyar Hala ne, mijin Hala Abu Hindu ne babansu (ba Annabi(saw) ba).


ﺭﺳﺎﻟﺔ ﺣﻮﻝ ﺑﻨﺎﺕ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص)، ﻣﻄﺒﻮﻋﺔ ﻁ ﺣﺠﺮﻳﺔ ﻓﻲ ﺁﺧﺮ ﻣﻜﺎﺭﻡ ﺍﻷﺧﻼﻕ ﺹ 6.


ﺟﻌﻔﺮ ﻣﺮﺗﻀﻰ ﺍﻟﻌﺎﻣﻠﻲ، ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﻣﻦ ﺳﻴﺮﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻷﻋﻈﻢ ، ﺝ 2 ، ﺹ .115 ﻧﻘﻼً ﻋﻦ ﺍﻟﺴﻴﺮﺓ ﺍﻟﺤﻠﺒﻴﺔ، ﺝ 1 ، ﺹ 140 ؛ ﺗﻬﺬﻳﺐ ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺩﻣﺸﻖ، ﺝ 1 ، ﺹ 303 ؛ ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﺨﻤﻴﺲ، ﺝ 1 ، ﺹ .264...


Kenan RUKAYYA da ZAINAB ba 'ya'yan Annabi Muhammad(saw) bane, kuma ba 'ya'yan Sayyidah Khadijah(as) ba ne, 'ya'yan kishiyar 'yar uwar Sayyidah Khadijah(as) ne, mai suna; Hala.


Dukkan malaman Tafsiri, Hadisi da As-babun-Nuzul sunyi tarayya akan cewa dalilin da yasa aka saukar da Suratul-Kausar shine; lokacin 'ya'yan Annabi Muhammad(saw) suka rasu, ya zama bashida sauran wani da ko daya, sai Ass Bin Wa'il As-Sahami (jigo a cikin Banu Ummayya) yake cewa da Quraishawa; su daina kula Annabi(saw) sabida mai yankakken baya ne (baya da magaji), da zarar ya mutu shikenan ba mai gadonsa. Sai Allah ya aiko Mala'ika Jibril(as) da Suratul-Kasaur.


أخبرنا محمد بن موسى بن الفضل أخبرنا محمد بن يعقوب أخبرنا أحمد بن عبد الجبار أخبرنا يونس بن بكير عن محمد بن إسحاق قال: حدثني يزيد بن رومان قال: كان العاص بن وائل السهمي إذا ذكر رسول الله(ص) قال: دعوه فإنما هو رجل أبتر لا عقب له لو هلك انقطع ذكره واسترحتم منه فأنزل الله تعالى في ذلك " إِنّا أَعطَيناكَ الكَوثَرَ " إلى آخر السورة.


ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ، ﺟﻼﻝ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﺍﻟﺪﺭ ﺍﻟﻤﻨﺜﻮﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻔﺴﻴﺮ ﺑﺎﻟﻤﺄﺛﻮﺭ، ﻣﺮﻛﺰ ﻫﺠﺮ ﻟﻠﺒﺤﻮﺙ ﻭﺍﻟﺪﺭﺍﺳﺎﺕ ﺍﻟﻌﺮﺑﻴﺔ ﻭﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ، ﻁ 1، ﺍﻟﻘﺎﻫﺮﺓ ـ ﻣﺼﺮ، 1424 ﻫـ.


Wannan hadisi na Ibn Abbas akan cewa dalilin saukar Suratul-Kausar shine; gorin rashin magaji da kafiran Quraishawa suka yiwa Annabi(saw). Kacokaf din malaman Tafsir, Hadisi da As-babun-Nuzul ba wani malami da bai ambaci wannan riwayar ba. Kama daga kan Suyudi a Tafsirul-Jalalain da Durul-Mansur, har zuwa kan Dabari a Tafsirul-Kabir, hakama Ibn Kasir, Fakhruddeen Razi, Qurdabi, kai har Abubakar Gumi (jagoran Izala) a Tafsirinsa 'Raddul-ahzan', duk sun yi tarayya akan cewa; dalilin gorin rashin magaji da aka yiwa Annabi(saw) ne yasa aka saukar da Suratul-Kausar.


ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ، ﺍﻟﺪﺭﺍﻟﻤﻨﺜﻮﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻔﺴﻴﺮ ﺑﺎﻟﻤﺄﺛﻮﺭ، ﺝ 10، ﺹ.707.


Malaman Tarihi sun tabbatar mana da cewa sai bayan saukar da Suratul-Kausar ne aka haifi Fatimah Az-Zahra(as), kuma ita kadai ce tal a 'ya'yan Annabi(saw) da zuriyarsa ta wanzu har yanzu, doriya akan cewa Fatimah(as) ce Uwar Imamai(as), kuma babu wani jinin Annabi(saw) (Sharif / Sayyid) a yanzu da ba ta hanyar Fatimah(as) nasabarsa take tukewa ba. Kenan tahanyar Fatimah(as) ce yasa Annabi(saw) bai zama mai yankakken baya ba? Sabida haka Fatimah(as) itace Kausar din da Allah ya bawa Annabi(saw) a wannan surar.


ﺍﻷﻟﻮﺳﻲ، ﺷﻬﺎﺏ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻟﺒﻐﺪﺍﺩﻱ، ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺭﻭﺡ ﺍﻟﻤﻌﺎﻧﻲ، ﺩﺍﺭ ﺇﺣﻴﺎﺀ ﺍﻟﺘﺮﺍﺙ ﺍﻟﻌﺮﺑﻲ، ﺑﻴﺮﻭﺕ ـ ﻟﺒﻨﺎﻥ.


Idan har Zainab da Rukayya 'ya'yan Annabi(saw) ne, kenan sun girmi Az-Zahra(as)? Idan sun girmi Az-Zahra(as), kenan sun rasu  kafin a haifi Az-Zahra(as)? To taya suka auri Usman Dan Affan a Madinah? Idan Az-Zahra(as) ta girmesu, kenan su basu haihu da Usman ba? Idan sun haihu, me ya sa babu Sharifai ko jinin Annabi(saw) da suke jingina kansu da RUKAYYA ko ZAINAB?


ﺭﺳﺎﻟﺔ ﺣﻮﻝ ﺑﻨﺎﺕ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص)، ﻣﻄﺒﻮﻋﺔ ﻁ ﺣﺠﺮﻳﺔ ﻓﻲ ﺁﺧﺮ ﻣﻜﺎﺭﻡ ﺍﻷﺧﻼﻕ ﺹ 6.


Da gaske malaman tafsiri sun kawo ma'anoni da yawa akan kalmar Kausar, misali, Ar-Razi ya kawo ma'nonin Kalmar Kausar fiye da 26. Mafi rinjaye daga cikin ma'anonin akwai cewa kalmar Kausar tana nufin Fatimah(as) ko kuma koramar Al-Kausara.


ﺍﻟﺮﺍﺯﻱ، ﺗﻔﺴﻴﺮﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ، ﺝ 10 ، ﺹ .333.


Bamu ce ba wata korama a Al-Jannah mai suna Kausar ba, amma ba itace aka ambata a Suratul-Kausar ba, dalili shine, menene hikimar ayi Annabi(saw) gorin rashin magaji, har a kirashi da mai yankakken baya, amadadin Allah yace ya bashi magaji sai kawai yace ya bashi koramar ruwa? Shin wannan zai iya kawar da gorin rashin magajin da aka masa? Doriya akan cewa su wadan da suka yiwa Annabi(saw) gorin rashin magaji, basu yarda ma akwai Allah ba, ballema su yarda akwai Al-jannah da wata koramar Kausara. Ga Quraishawa don ance an bawa Annabi(saw) koramar ruwa amadadin gorin da suka yimasa, wannan ma ai abin dariya ne.


ﺍﻟﺮﺍﺯﻱ، ﻓﺨﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﻣﻔﺎﺗﻴﺢ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﺍﻭ ﺍﻟﺘﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ، ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻔﻜﺮ، ﻁ 1، 1401 ﻫـ. ﺍﻟﻤﺮﺍﻏﻲ، ﺃﺣﻤﺪ ﻣﺼﻄﻔﻰ، ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻤﺮﺍﻏﻲ، ﺩﺍﺭ ﺇﺣﻴﺎﺀ ﺍﻟﺘﺮﺍﺙ ﺍﻟﻌﺮﺑﻲ، ﺑﻴﺮﻭﺕ ـ ﻟﺒﻨﺎﻥ.


Maganar gaskiya itace, Fatimah(as) ita ce Kausar, sabida ta hanyarta ne Allah ya arzirta Annabi(saw) da zuriya har yanzu, kuma har gobe akwai zuriyar Annabi(saw) a Duniya, ta hanyar tsatsun yarsa Fatimah(as).


ﺍﻟﻈﺎﻫﺮ ﻣﻦ ﻛﻠﻤﺔ ‏(ﺇﻧّﺎ ﺃﻋﻄﻴﻨﺎﻙ ﺍﻟﻜﻮﺛﺮ‏) ﻫﻮ ﺃﻥّ ﺍﻟﻠﻪ ﻋَﺰَّ ﻭﺟَﻞَّ ﺳَﻴﺮﺯُﻕُ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻣﻦ ﺑﺮﻛﺔ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺒﻨﺖ ﺍﻟﻄﺎﻫﺮﺓ ﻧﺴﻼً ﻓﻲ ﻏﺎﻳﺔ ﺍﻟﻜﺜﺮﺓ، ﻻ ﻳﻨﻘﻄﻊ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ، ﻭﺇﻥ ﺍﺳﻤﻪ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﺳﻴﺒﻘﻰ ﺣﻴﺎً ﻭﻣﺘﺄﻟﻘﺎً ﻋﻠﻰ ﻣﺮِّ ﺍﻟﻌﺼﻮﺭ .


ﺍﻟﻄﺒﺎﻃﺒﺎﺋﻲ، ﺗﻔﺴﻴﺮﺍﻟﻤﻴﺰﺍﻥ، ﺝ 20، ص 431.


Hadisai sun inganta, Annabi(saw) yana cewa;


‏ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻣﻦ ﺃﺷﺠﺎﺭ ﺷﺘﻰ، ﻭﺧﻠﻘﺖ ﺃﻧﺎ ﻭﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻣﻦ ﺷﺠﺮﺓ ﻭﺍﺣﺪﺓ، ﻓﻤﺎ ﻗﻮﻟﻜﻢ ﻣﻦ ﺷﺠﺮﺓ ﺃﻧﺎ ﺃﺻﻠﻬﺎ، ﻭﻓﺎﻃﻤﺔ ﻓﺮﻋﻬﺎ، ﻭﻋﻠﻲ ﻟﻘﺎﺣﻬﺎ، ﻭﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺛﻤﺮﺗﻬﺎ...


"Duk mutane an haliccesu daga tsatso mabambanta, amma ni (Annabi(saw) da Ali(as) daga tsatso daya muke, ba wani tsatso (mai albarka) da yakai ga tsatson da nine asalinsa, Fatimah(as) ce rashensa, Ali(as) ne tushensa, Hasan(as) da Husain(as) ne yayan itacensa".


ﺍﻟﻄﺒﺮﺳﻲ،ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺟﻮﺍﻣﻊ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ، ﺝ 3 ، ﺹ .856، ﺝ 10، ﺹ .835. ﺍﻟﺸﻴﺮﺍﺯﻱ، ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻷﻣﺜﻞ، ﺝ 20، ﺹ 498.


A wannan hadisin Annabi(saw) ya nuna mana cewa tsatsonsa zai wanzu ne ta hanyar Fatimah(as) da Ali(as). Wannan hadisin ya tabbatar mana cewa; duk fadin Duniya a yanzu ba wani jinin Annabi(saw) wanda ba daga Fatimah(as) ba ne.


 ﻭﻫﻜﺬﺍ ﻛﺎﻥ ﻧﺴﻞ ﻋﻠﻲ ﻭﻓﺎﻃﻤﺔ ﻧﺴﻼ ﻣﺒﺎﺭﻛﺎ ﻟﻠﻨﺒﻲ(ﺻ) ﻭﻫﻜﺬﺍ ﻛﺎﻥ ﺃﺑﻨﺎﺀ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺟﻤﻴﻌﻬﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﺎﺩﺓ، ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺗﺮﺟﻊ ﺃﺻﻮﻟﻬﻢ ﺇﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ﺻ). ﺇﻥ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺴﻼﻟﺔ ﺍﻟﻤﺤﻤﺪﻳﺔ ﺍﻟﻄﻴﺒﺔ ﻭﻟﻢ ﺗﻨﻘﻄﻊ ﻓﻲ ﺃﻱّ ﻭﻗﺖ ﻣﻦ ﺍﻷﻭﻗﺎﺕ، ﺑﻞ ﺇﻧّﻬﺎ ﻣﻨﺘﺸﺮﺓ ﻓﻲ ﻛﻞ ﺑﻘﺎﻉ ﺍﻷﺭﺽ...


Kuma wannan tsatson mai Albarka zai cigaba da wanzuwa har ranar tashin Qiyama. Kenan yarda da Fatimah(as) ce Kausar shine hakikar kawar da gorin rashin magaji da aka yiwa Annabi(saw).


ﺍﻟﻤﺮﺍﻏﻲ، ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻤﺮﺍﻏﻲ، ﺝ 30 ﺹ 253. ﺍﻟﺮﺍﺯﻱ، ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ ﺍﺑﻦ ﺇﺩﺭﻳﺲ، ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ، ﻣﻜﺘﺒﺔ ﻧﺰﺍﺭ ﻣﺼﻄﻔﻰ ﺍﻟﺒﺎﺯ، ﻣﻜﺔ ﺍﻟﻤﻜﺮﺓ.


Fadar Allah(t) a kashen surar, cewa;


إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ


"Mai maka gorin rashin magaji; shine marar magaji kuma mai yankakken baya".


Wannan ayar ta tabbata mana cewa Fatimah(as) ce Kausar. A yanzu ba Ass Bin Wa'il ba, kacokaf din Bunu Ummayya bayansu ya yanke, a yanzu ba mai raya shi jinin Bunu Ummayya ne a nasaba. Amma akwai miliyoyin jinin Annabi(saw) a dukkan Nahiyoyin Duniya; kama daga Gabas ta tsakiya (middle east) Asia, Afrika da Turai (Europe) da Amurka, kuma duk tahanyar 'yarsa Az-Zahra(as), idan Annabi(saw) yana da wasu 'ya'yan banda Az-Zahra(as), kuma har sunyi aure sun haihu, me ya sa ba jinin Annabi(saw) ta tsatsonsu?


ﺍﻟﻄﺒﺮﺳﻲ، ﺃﺑﻲ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﻔﻀﻞ ﺑﻦ ﺣﺴﻦ، ﻣﺠﻤﻊ ﺍﻟﺒﻴﺎﻥ ﻓﻲ ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ، ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻤﻌﺮﻓﺔ.


Tayiwu wani yace; to ai Annabi(saw) Balarabe ne, ya akayi aka samu jininsa a wajen Larabawa? Sai muce, sabida hadakar aure tsakanin Larabawa da wadanda ba larabawa ba. Doriya akan cutarwar da aka yiwa zuriyar Annabi(saw) a bayansa(saw); wanda hakan ya cilasta masu hijira daga kasashen Larabawa zuwa Nahiyoyin Duniya.


ﺭﺳﺎﻟﺔ ﺣﻮﻝ ﺑﻨﺎﺕ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص)، ﻣﻄﺒﻮﻋﺔ ﻁ ﺣﺠﺮﻳﺔ ﻓﻲ ﺁﺧﺮ ﻣﻜﺎﺭﻡ ﺍﻷﺧﻼﻕ ﺹ 6. ﺍﻟﺸﻴﺮﺍﺯﻱ، ﻧﺎﺻﺮ ﻣﻜﺎﺭﻡ، ﺍﻷﻣﺜﻞ ﻓﻲ ﺗﻔﺴﻴﺮ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻤﻨﺰﻝ، ﺩﺍﺭ ﺇﺣﻴﺎﺀ ﺍﻟﺘﺮﺍﺙ ﺍﻟﻌﺮﺑﻲ، ﻁ 1، ﺑﻴﺮﻭﺕ ـ ﻟﺒﻨﺎﻥ، 2002 ﻡ.


Ya Allah! ka barmu da kaunar Fatimah(as), Babanta(saw), Mijinta(as) da 'Yayanta(as). Ya Allah! Albarkacinsu ka yarda damu, ka yarda da ayukanmu, ka biya mana bukatunmu, kasa Al-Jannah firdausi ce makomarmu!!


Sani Muh'd Sani Muh'd 

Baban humaid Mnnu//Ng0027

@-ma'asumah Nigerian News update



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post