KA JI SIFFAR SALLAR MALA'IKU ABABEN KARRAMAWA !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
IDAN NAYI IRINTA NA FI SAMUN NUTSUWA CIKIN SALLAH TA
Karatu da bincike na da dadi musamman ma idan akan addinin muslimci ne. Yanzu sallar jama'a ta zama abinda ake yi kawai na ra'ayi da son zuciya, domin tuntuni an kaucewa siffar yadda Annabi (S.A.W.W)ke yin sallarsa.
Idan kana yawo cikin birni da qauye za ka riqa ganin salloli jaka-kala, wani ya rungume qirjinsa, wani ya kama cikinsa, wani ya sake hannayensa, wani kuma ya kama qwabrinsa (leg)yayin ruku'u, kuma wai duk hakan ana yin koyi da Manzon Allah (S.A.W.W)ne, har ma ka raasa fa'idar da ke cikin hakan.
Bari dai mu kawi haqiqanin siffar sallar fa Mala'ika Jibril (A.S)ya koyar da Manzon Allah (S.A.W.W).
YADDA JIBRIL (A.S)YA KOYAR DA MANZON ALLAH (S.A.W.W)
Ibn Abiy Hateem ya riwaito, kuma Hakeem Annaisaburi ma ya riwaito cikin Mustadrak nasa cewa;
Wahabin Bn Sulaiman Alqadhiy ya bamu labari cikin shekara ta 255, Isra'il Bn Hateem Al-Maruziy ya bamu labari, Muqatil Bn Hayyan ya bamu labari daga Asbagh Bn Nabatata, daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A.S)yace; Yayin da wannan surah ta sauko ga Annabi (S.A.W.W);
" INNAH A'ADAINAKAL KAUTHAR. FASALLI RABBIKA WAN NAHR ". Sai Manzon Allah (S.A.W.W)yace;
" Yaa Jibrilu, wanne irin suka ne Ubangijina yake umartata da shi "? Sai yace;
" BA SUKA BANE, SAI DAI SHI YANA UMARTARKA NE IDAN KAYI HARAMAR SALLAH JA 'DAGA HANNAYENKA YAYIN KABBARA, DA YAYIN RUKU'U, DA YAYIN 'DAGOWAR KANKA DAGA RUKU'U, DA YAYIN SUJJADAH, DOMIN ITA CE (siffar)SALLARMU DA KUMA SALLAR MALA'IKUN DA KE CIKIN SAMMAI BAKWAI.
LALLE GA KOWANNE ABU YANA DA ADO, KUMA ADON SALLAH SHINE 'DAGA HANNAYE YAYIN KOWACCE KABBARA ".
Wallahi duk lokacin da nayi sallah irin wannan siffa na kan ji nutsuwa tare da yaqinin karbuwarta.
DA FATAN ZA KU DAWO KAN SIFFAR YADDA ANNABI (S.A.W.)KE YIN SALLARSA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah GGuda.
~ 12th December, 2019.

Nikuma da sallah nakeyi batare da daga hannu ba soboda ban sami cikakken bayani ba sai yanzu allah yasaka maka
ReplyDelete