Shin ko kun San Da Wannan ???
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
@Shafi Domin Kai Da Al'ummar ka
_______________________________
DUK ABINDA YA SAMI MUMINI ALKHAIRI NE
Babu shakka idan abu na cutarwa ya sami mutum yakan ji ciwo , musamman ma idan an yi masa cutarwar ne bisa zalunci ba bisa kuskure ba.
Waqiar Zaria wacce ta auku ranar 12-12-2015 ta samar da wasu nasarori ga harka islamiyyah wadanda ba a zaci hakan ba, domin an yi ta ne don shafin yunqurin gwagwarmayar muslimci wacce Sayyid Zakzaky (H )ke jagoranta.
Daga cikin nasarorin sune:-
(1)- HARKA TA TUNBAZA :- Wadanda suka afkar da wannan waqi'a ba su zaci cewa kiran zai ratsa sassan guraren da bai ratsa ba.
(2)- AMSA KIRA:- Bisa qiyasin da ake yi shine , sakamakon wannan waqi'a an rasa rayuka 1000, sai dai kuma wadanda suka amsa wannan kira bayan waqi'ar ba a san adadin yawansu ba, domin nunkin-banunkin aka samu.
(3)- TA BAYYANA SAYYID (H )MALAMIN DUNIYA NE:- Da ace kafin zuwan waqi'ar za ace wannan malamin fa malamin duniya kaf ba na Nigeria kadai ba da wasu za su qaryata, amma faruwarta sai ya tabbatarwa duniya cewa Sayyid (H )malamin duniya baki daya , domin duniyar ta amsa cewa nata ne.
(4)- AZZALUMAI SUN QASQANTA :- A nufin azzalumai sun yi zaton cewa za su iya yin yaqi da gaskiya ne tare da murqushe ta, amma sai ta bayyana cewa ba a kauda gaskiya da bakin bindiga !
(5)- SAMUN IZZAH :- A yanzu duk inda almajirin sayyid (H )yake yana da izza wajen azzalumai da 'yan barandarsu, domin an san ba sa daukar zilla.
(6)- JAMA'AH SUN FAHINCI CEWA BUHARI AZZALUMI NE :- Wasu sunyi kusan rasa imaninsu ta hanyar bawa Buhari kalmar adala , amma yanzu kowa yasan shi azzalumi ne.
(7)- TA BAYYANA CEWA 'YAN SHI'AH MASU BIN DOKA NE :- A da fassarar da ake yiwa 'yan shi'ah shine ba sa bin doka da oda, sai ga shi ta bayyana qarara cewa ashe sune ma masu bin doka, domin har dokar kotu ta shaide su a matsayin masu bin doka wadanda aka zalunta .
(8)- SAMUN YAQINI NA CEWA AKAN GASKIYA MU KE:- Duk da cewa muna da yaqini kan wannan tafiya, amma faruwar hakan ya qara mana yaqini kan wanda muke da shi, domin mun ga irin abinda ya sami Annabawa (A.S )ne ya same mu.
(9)- AN GANO MAKIRCIN GWAMNATI:- Wannan waqi'a ta fitar mana da irin makircin da gwamnati ke yi cikin harka islamiyyah don ta rusa da'awar ta hanyan yin amfani da yaranta wadanda ta shigar da su don yi mata aiki.
(10)- AN GANO MAQIYAN DA AKE TARE DA MU :- Sakamakon wannan waqi'ah an gano maqiyan da ake tare da su wadanda ke farin ciki da abinda yake samun mu, wadanda a can baya muke daukar su masoyan mu.
D.S
Tare da Ado Isah Guda .
~ 13th December, 2019.
