Cikin dare Imam Yayi Masu Jawabi saboda yasan akwai wadanda suka biyoshi da fatan zasu samu daukaka !!!


Lokacin da Mutane suka fuskanci Abinnan Izzah ne Wato Daukaka ne, Abin kamar ya Riga ya tabbata ne. Shikenan kowa Sai yace eh, dashi ne. Amma in suka fuskanci Abin ya zama Mutuwa ko wahala to nan Zakaga An zame.*
-Sheikh Ibrahim Zakzaky Rufe Taron Ijtima 1992.
.
Shige Irin Wannan ne ya auku a daren Ashura ga Imam Hussaini. A karbala Wanda lokacin Yasan cewa da yawa Mutane Sun bishi akan cewa Shine zai zama Shugaba sukuma zasu zama Manyan Mutane na kusa-kusa dashi, to gashi kuma ya tabbata Al'amari ya canza ya zama Mutuwa. Saboda haka cikin dare Imam Yayi Masu Jawabi saboda yasan akwai wadanda suka biyoshi da fatan zasu samu daukaka ne, to ga Makomar Abinda ya faru da Musulum bin Akil yakasance, da Makomar Khani bin Urwa, wani Malami a khufa, da Makomar Khais bin Musakha, Wanda Manzon Shi Imam Hussain ne, da kuma sauran Mutane wadanda sassaresu akayi wasu a kasuwa aka tsitsiresu aka aika da kawukansu. Yace to duk wanda yake bukatar Makoma Wadda ba Irin Wannan ba to wannan dare yayi Masa sutura sai ya sulale, to yale kuwa Wasu sunka sulale, Sai suka ta tsiyayewa kawai Shikenan sai yazan suka Rabuda wadanda suka yadda Makomarsu ta kasance Hakanan . kuma haka makomar tasu ta kasance.

To Idan Mutane suka Fahimci Abinnan kamar ya rigama ya kafu in ba'ayi dakai ba za'abarka abaya Ayi baka to sai suce damu aciki har su cika baki, In aka kawo Jarabawa domin Wannan Jarabawa ce daga Allah. don dama Allah ne yake tabbatar da Abu ko kuma yazan bai tabbata ba, don Abin yana hannunsa ne, ba yawan Jama'a ne ko wani abu ba, karfi na Allah ne. Idan Mutane Suka Raja'a ga Abu In jarabawa tazo Sai a girgizasu har su dauka abin ya kawo karshe . kamar yadda aka girgiza na farko a karon Khandak, *"Dayawa wasu sun dauka abin yakawo karshe"*  duk dayake da can farko tuntuni nasarori ake ta samu , amma wannan lokacin sai suka dauka an mutu kawai, sai ko wasu suka fara tsiyayewa, sannan a karshe  Sai Allah yayi Abin. Yazamana ma ko kwamawa ba'ayi ba Allah ya Isarwa Muminai yakin, yazamana  ko sara basuyi ba, kawai shi sai yayi Masu yakin. Amma bayan da ya jaraba Muminai. Ya tace na tacewa Muminai wadanda Suka ragu da Imani sai yayi Masu yakin batare da sunyi ba.

To Irin wannan na baku misali ne  cewa ana tafiya dinnan wata rana  wata Jarabawa zata bijiro ko bata 'yan Sara suka ba.  Kamar Misali a *makarfi da kudan* yan Sara suka wadanda suka dauka Abin ya kare. Musamman ma a kudan, Wanda ainahin kafin Zuwan mu garin Mutum biyu basu  maganar abinda ya auku ba,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post