Fa'idojin Auren 'Yar Kauye !!!



'YAR QAUYE BA BAQAUYIYA BA

Qauye mazauni ne na rayuwar al'umma wanda ke dauke da qarancin jama'a da kuma qarancin kayan more rayuwa. Yawancin irin abinda ake samuw don more rayuwa ba a cika samu a irin wadannan gurare ba. Misali:-

-Wutar lantarki (Nepa)

-Hanya (kwalta).

'Ya qauye kuma ita ce wacce ke zaune a irin wannan guri da muka bada misali a kansa, ko da kuwa tana da ilimin addini dana zamani, domin wani lokaci akan sami irin su cikin wannan guri.

Ita kuma baqauyiya ana samunta cikin kowanne irin guri wanda jama'a ke rayuwa, wato cikin birni da qauye kamar yadda ake samun wayayyi ya/mai ilimi a kowanne guri.

Daga ciki  fa'idojin auren 'yar qauye akwai:-

(1)- SAURIN GODIYA:- Za ka same ta da yawan godiya cikin kyautatawar da mijinta ke yi mata.

(2)- BIYAYYA:- Yawancin 'yan qauye suna da biyayya, domin suna samu daga mahaifansu ba tare da nuna girman kai ba.

(3)- RASHIN BURI:- A rayuwarsu sukan gamsu da abu qanqani sabanin yadda 'yan maraya ke yi ko da kuwa iyayensu ba kowa/komai bane.

(4)- TARBIYYAH:- Yadda suke ganin girman dukkan na sama da su tare da nuna kunya cikin dukkan al'amransu.

(5)- SAUQIN SARRAFAWA:- Da shike ba su duniya da fadi (wide) ba za ka tarar dasu babu girman kai, saboda haka yadda kaso da su haka za kayi da su ko haka za suyi maka ba tare da bijirewa ba.

Wadannan dalilai yasa za kaga manyan masu kudi da malamai suna shiga qauye don neman matar aure, domin tarbiyya da kunya na qauye. Manzon Allah (S.A W W) babban misali ne.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 4th November, 2019.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Hakika wannan gaskiya ne domin ni na jarabta na Kuma tabbatarda haka

    ReplyDelete
Previous Post Next Post