Daga maganganun hikima na Imam Aliy (as)!!


Duk Wanda yakaranta zai fa'idantu..

Cikin maganganunsa na hikima (A.S) yana cewa;

(1)- " KA CIGABA DA KYAUTATAWA BAYIN ALLAH KO DA BA SA GODE MAKA, DOMIN TANA YIWUWA WANDA MA BAI AMFANA DAGA GARE KA BA YANA MADALLAH DA AIKINKA, GA SHI KUMA ALLAH NA SON MASU KYAUTATAWA  ."

          SHARHI
         ________

Shi aikin alkhairi ba ana yin sa ne don mutane su gode maka ko kuma su yabe ka ba, a'a, ana yinsa ne kawai don neman yardar Allah.

Saboda haka duk abinda za kayi na kyautatawa kada ka damu da cewa lalle sai wanda ka kyautatawa ya gode maka. Shi aikin alkhairi ba ya buya, matuqar ka yi shi za ka ji ana ambatonsa daga bakin wadanda ba su ka riwa ba.

Sannan kuma matuqar kana kyautatawa Allah zai hada ka da wasu bayin Allah wadanda su ma za su kyautata mata ba tare da ka yi musu wani abin kyautatawa gare su ba.

Babbar ribar kuma ita ce samun yardar Allah, wanda idan ya yarda da kai Uban kowa ma ya qi ka, domin Shi (Allah) na son masu kyautatawa.

Ka ga kuwa duk wanda Allah ke son sa ba zai tozarta ba a duniya da kuma lahira.

Za mu cigaba insha Allah.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08126385470-- 07059911360

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post