DAGA MAGANGANUN HIKIMA NA IMAM ALI (A S) !!! (2)



DUK WANDA YA KARANTA ZAI FA'IDANTU

Cikin maganganunsa na hikima (A.S) yana cewa;

" ILIMI YANA TATTARE DA AIKI, WANDA YA KE DA ILIMI SHI AKA FI SANI DA AIKI, DOMIN ILIMI YANA KIRAN MA'ABUCINSA GA AIKI. IDAN YA AMSA KOMAI ZAI TAFI DAIDAI, IDAN KUMA YA QI AMSAWA SAI ILIMIN YA TAFI ABINSA."

        SHARHI
      _________

Ashe tarin karatu ba komai bane matuqar anqi yin aiki da shi, yin aiki da abinda aka karanta shine ilimi. Wanda ke da ilimi a gunsa ya kamata ace anga aiki, idan kuma ba ya aiki da shi sai ilimin ya tafi ya bar shi ba mutunci.

Wannan dalili yasa mafi yawa daga cikin masu da'awa a matsayin su na jagorori suka zama tamkar bawon dabino wanda ba shi da amfani ga mutum.

Maimakon suyi abinda zai amfanar dasu sai dai kaga sun zama fitina cikin al'umma, domin babu ilimi sai dai haddasa gaba cikin musulmai da cusa musu qiyayyar juna, kamar dai yadda Shaidan (Satan) ya kasance.

Yaa Allah ka amfanar damu daga wannan magana ta tsarkakekken bawanka (A.S).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

  08126385470--08137925034

~ 7th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post