Ana Sanya shine Cikin Babin Halasci.
Jahilci ciwo ne mai wuyar magancewa matuqar ba ayi sa'ar doruwa kan maganin da zai magance shi ba. Wannan magani kuwa shine sahihin ilimi ba gurbatacce ba, wanda ke saurin magance wannan cuta ta jahilci.
Da yawa mutane ba sa iya bambance tsakanin ayyukan addini da kuma abinda ake kira halas cikin addini.
Ayyukan addini shine dukkan wani aiki wanda in ka aikata shi bisa yadda addini ya koyar za ka sami lada, sannan kuma ko da ace ba ka sami zunubi ba sakamakon rashin yin sa kamar yadda shari'a ta koyar ba, to, ba za ka sami lada ba.
Halas kuma shine dukkan abinda ba za ka sami zunubi ba ta hanyar rashin aikata shi, kuma ba a ba ka lada don ka aikata.
Ko da ta hanyar kuskuren rubutu ne ko kuma tuntuben harshe ba a taba samun guri daya (1) da aka nuna cewa buga Badujala na daga cikin ayyukan addini ba ballantana ace ga misalin girman ladan sa in an aikata ba.
Shi dai wani aiki ne da ake sanya shi cikin babin ayyukan halasci, tamkar dai ruwan sa ne ga mai buqata, ko kuma abinci ga mai jin yunwa. Idan kaga dama za ka iya bugawa, idan kuma kaga dama sai ka bar shi.
Amma an sami gungun wasu jahilai da ke qalubalantarsa da cewa wai ba ya daga cikin ayyukan addini, alhali ba su taba ji wani ya kira shi da aikin addini ba.
Wannan furuci nasu ya yi kama da wanda zai fito yana cewa, AI AMFANI DA LOUD 🔊 SPEAKER 📢 BA YA CIKIN AYYUKAN ADDINI !
Duk wanda ya yi wannan furuci ya fi kama da ka kira shi wawa daqiqi !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 16th November, 2019.
Tags:
Tunatarwa

Kano ta fara daukar harami sakamakon murnar ranar taku taha
ReplyDeleteAslm I muku fatan alhairi.
ReplyDelete