⇀Yanzu ashe in da abin in tambaye ku ne, wanne ya fi sauqi a canza,
Makkan lokacin Annabi ko Nijeriyar yanzu? Nijeriyar yanzu ya fi sauqi.
⇀
Amma in Annabi ya zama aikinsa ne ya canza kuma ya canza wancan al’ummar, mu yanzu meye namu uzurin? Ko kamar yadda na ce, ko kuma an ce mana ne ai ‘optional’ ne? In ka ga dama ka yi ko kar ka yi?
⇀Ko kuwa an ce mana ne a wani zamani an dauke mana wannan takalifin, sai wasu ’ya’yanmu da jikokinmu da za a haifa nan gaba in Mahadi ya
bayyana, sune Allah ya dora masu banda mu? Duk ina tambayoyi ne,
kun san kuma ba su da amsa.
⇀To idan kuwa duk haka nan ne, to menene matsayinmu gobe
qiyama in muka tsaya gaba ga Allah? Mu ce mene? Akwai wani uzuri
ne? To, shi ne zancen.
⇀Ba zancen a yi tarihin Annabi bane, a dinga jin dadi. A ce Annabi ya ci uban wuya, ya sha wahala, an yi masa rotsi, an cire masa haqori, an yi masa kaza.
⇀An daidaice shi an yi masa ruwan
kibau, an kore shi, an menene, an menene. Ka rubuta, ka yi bayani, ka yi
sharhi, ka zama Shaikh, ko a ba ka satifiket. Yanzu batun al’umma a aikace, mu me muke yi? Kai me kake da
shi wanda za ka je da shi gobe qiyama, guzurinka na aiki da ka yi?
⇀Ko za ka je da satifiket din ka ne ko ‘Research’ din ka? Ka ce ai ka bincika ka ga lallai su musulmin farko sun sha wahala!? Sun yi aiki ne. Amma kai fa? Kai ko zafin rana ma ba ka daurewa.
⇀To, shi ne tambayar, na ji an
yi shiru. A taqaice abin da nake cewa shi ne wannan wajibinmu ne kuma Allah ya dora mana ne, aikin da ya zama dole mu yi ne, kuma za a tambaye mu gobe qiyama.
⇀Ga shi dai muna ganin ana mana dauki dai-dai, kafin ’yan shekaru qalilan duk wanda ke nan za ka gan shi ba shi. Duk komawa wajen taro za a yi. Kuma ranar taro za a tattaro mu a jero mu ne, qarni bayan qarni, al’umma bayan al’umma.
⇀Mu da muke wannan zamanin, a wannan lokacin za a tambaye mu, me muka yi a namu muhallin? Wannan kuma aiki ne namu mu duka, ba na wasu mutane bane. Fakam da yawa idan ana magana sai ka ga wani yana qoqarin ya zuqe ya ce ai shi banda shi a wannan aikin.
⇀Ko ya ce na Malamai ne, ko ya ce na Sarakai ne. To aiki ne na kowa da kowa. Kowa da irin gudummawar da zai bayar! To, amma mu zo mu dubi kanmu, wai ba ma yin komai ne? Kawai muna zaune ne muna yin wani aiki, mummunan aiki, ‘negetive work?’
⇀Tambaya, ba ma aikin komai ne? Muna aiki! Wane irin aiki? Mu kenan muna ta rikici, muna ta rikici da junanmu.
⇀Daga Jawabin Sayyid Zakzaky (H) a Mauloud din Manzon Allah (S) shekarar 2008, Hijira 1428.
