Amshi::
Imam Taka da Lafiya Al'Zakzaky Ibrahimu Saduki kake, Ki Gudu mai Sanya Mazaje gudu.
__________________________
part 1
Allahu al maliku qawuyyu da yai duniya,
Shi yai yo mu kasa kasa ciki yayi Najeriya,
Biranenmu iri iri cikinsu yayo zariya,
Rana ce mai haska ko ina fadin duniya,
Shine Sayyid Zakzaky haifeffen Zariya,
Kafin mu nutsa Rabbana salati karka tsaya,
Wurin Sidi Muhammadu da alaye bai daya,
Kasa Sayyid Zakzakyu jininsa dake duniya,
Ansarul Imam Mahdiyu mai gyaran tarbiya,
Lallai shi sirrin nabiyune asalin tarbiya,
Shiri na Ilahu Imamu mai haskaka nahiya,
Na karshen duk aulaya une bawani fariya,
Takobi daga Rabbu maganin 'ya'yan Fariya,
Ruwa mai kautar da dukka dauda mai gaskiya,
KARANTA WASU LABARAI; Isah Almasihu zai dawo domin yin wasu ayyukka biyu!!
Tudu kake ka zarce gangara baba gwagwarmaya,Kowa a kasar nan da arzikinka yake tutiya,
Kaine gata nasa zahiri koda yakiya,
Da kai Allah zaya gyara dukkan duniyaaa,
Taku naka dai dai Imamu munbika gaba daya.
KO ZAKA IYA YIWA SAYYID (H) BAITY BIYU ANAN ACIKIN COMMENTS????
↑______________________↑
Daga Shafin [M.N.N.U=MA'ASUMIYA]
Tare da
Salisu Umar Mazajen Zakzakyya
08021395846
Tags:
Filin Mawaka
Taka lafiya mai turmuza hancin maqiya
ReplyDeleteLabbaika ya cikakken mai gaskiya
Gaisheka nake ya kogin shiriya
Allah yaja kwana ya kwana ya mai hana danniya
Allah ya qara lpy ya sarkin juriya
Kataka sannu sannu ya sarkin yafiya
Allah qara kariya ya jikan ausiya
Ilahi yaimana baiwa dakai dole muyi godiya
riobrachsponpi James Kava click
ReplyDeletealasweter