Baki ko alqalami ba zai iya bayyana haqiqanin wacece Sayyadah Zainab (S.A) ba, sai dai a ambaci wani abu daga ciki don haskakawa masu binciken saninta. MAHAIFINTA:- Shine Imam Ali (A.S), Bn Abu 'Dalib Bn Abdulmudallib (A S).
MAHAIFIYARTA:- Ita ce Sayyadah Fatimah (S A), 'yar fiyayyayen halitta Manzo (S.A.W.W) dan Abdullahi dan Abdulmudallib (A.S). Mun taqaita kan Abdulmudallib, domin cigaban zai kasance ne tamkar mun koma kawo sassalar Manzo (S). Ta kasance 'yar'uwa shaqiqiya wajen Imam Hassan da Hussaini (A S). Ta auri dan baffanta Abdullahi Bn Ja'afarul-'Dayy ar (A.S), wanda aka hana musu cin sadaqa saboda tsarkinsu. Ta haifa masa 'ya'ya kamar haka:- (1)- Aliyu (2)- Aunan, ana kiransa (Akbar). (3)- Abbas (4)- Muhammad da (5)- Ummu Khulthum. Zuriyarsu nanan ana samunsu har yanzu. Ta kasance tamkar Uwa ga Iyalan gidan Ma'aiki (S.A.W W), da kuma Sahabban Imam Hussaini (A.S) a filin Karbala. Ta gaji mahaifinta Imam Ali wajen jaruntaka da fasahar zance yayin magana. Ita ce ta yayewa Banu Umayyah zani a kasuwa ta hanyar bayyana matsayinsu (Ahlul-Bait), na kusancinsu ga fiyayyen halitta (S), tare da nuna cewa su Banu Umayyah azzalumai ne wadanda su kaci amanar Manzo (S) ta hanyar zubar da jinanan iyalan gidansa bayan wafatinsa. Akwaita da Balaaga wajen magana. Ta rera wata waqa cikin baqin ciki kamar haka; - Me za kuce yayin da Annabinku yace, - Me kuka aikata alhali kune qarshen al'umma, - Game da tsatsona da iyalina bayan na barku, - Daga cikinsu akwai ribatattu kuma daga cikinsu akwai wadanda aka jiqe da jini, - Me yasa wannan ya zama sakamakona yayin da nake yi muku nasiha, - Ku ka maye min da sharri cikin zuriyata?
Daga wakilanmu na Bauchi zone. Tare da Ado Isah Guda. 08137925034-08126385470
Tags:
Munasabobi