PELVIC INFLAMMATORY DISEASE (P. I. D)

   

Chuta da magani


Daga: ma'asumiya Nigeria News Updates


Tareda: Jibril Usman Sarki ( 08149953832)


Sau da yawa mata kanje asibiti idan lalura na damunsu sai  suji ana ce masu suna fama da P.I.D.ko kuma sunki samun ciki ko suna ta bari se ace ai P.I.D garesu.to wannan ne yasa nace to bara nai karin haske akan wannan cutar kowa ma ya santa

Wato P.I.D wata nau'in cuta ce dake kama mahifar mata kadai.sakamakon yaduwar kwayoyin cutar bacteria na saduwa wato STI.ita wannan cuta tana faruwa ne saka makon faruwar cutar sanyi ta gonoriya(wato cutar da ake dauka ta saduwa ba ta sanyi ba) ko kuma cutar chlymidia ko candidiasis da sauransu.wadan da sukan rayu ne a farjin mace.to idan su wadannan cutar misali ta gonoriya mace na dauke da ita sannan ba'ayi maganinta ba.to takan yadu ta bar farjin mace se ta gangara mahifa.se ta illata madaukan mahaifa ko (pollofian tube) ko kuma ta illata ita kanta mahaifar ko kuma ta illata su kwayoyin haihuwar mace(ovarries).to saka makon tashi da tayi daga farji zuwa mahifa to tabar nau'in kwayoyin cutar saduwa ta koma P.I.D.daga nan se mace ta fara jin wadannan alamun

-zafi yayin fitsari ko kuma yin fitsari dan kadan.
-zazzabi
-zafi yayin saduwa(sex)
-yawan yin al'ada cikin wata takan iya yi sau 2-3
-fitar farin ruwa marar dadi me wari.
-ciwon mara
-idan yayi karfi yana hifar da ciwon baya me tsanani

Sannan idan suka jima ajikin mace sukan haifar da barin ciki,rashin haihuwa da sauransu. Sbd haka wadan nan sune alamomin cutar ta p.I.d sannan wasu matan ma bazasu ji wadannan alamun ba musamman idan cutar chlamydia ta haifar da shi P.I.D din

To shawara anan dole se masu maganin gargajiya sun kiyaye dan su daina wahalar da mata na basu itace, kamata yai su turasu asibiti
Domin ganin masana akan abun.sannan mace ta lura  da taji sauyi a jikinta na wadannan alamun to tayi gaggawar zuwa asibiti  dan ganin masana cutar (likitoci.

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Ni naje asibiti wallahi nayi scanning nafarko ance Babu na biyu ance Babu sai a na ukku akace akwai duk waNi magani nayi nayi allura Amma daya daina sai yadawo.ance nida mijina zamuyi tashan magani Amma har yanzu bai dainaba😫

    ReplyDelete
  2. Nayi duk want jinyan asibiti Amma shiru

    ReplyDelete
Previous Post Next Post