Yi shere domin Wasu sugani Su Amfana
Mu tashi mu kwaci Kanmu akan al'amarin yan'cin Sheikh Zakzaky (H) da wannan mummunan bakin zaluncinda ake mana. Kowa yayima kansa kiyamul layli, a tashi ayi aiki tukuru, ahadu gaba daya a fuskanci wannan zaluncin da ma'abotansa. Kada dan'uwa ko yar'uwa su jira sai ance masu ga abinda za suyi sannan suyi. A wani abin zai iya zama hakanan, amma akan wannan gaskiya ba fa zai zama hakanan ba.
Kada daga baya muyi danasanin da ba haka mukayi ba, wannan bawan Allah yanada hakki akanmu da yakamata ace mune da kanmu za muyima kanmu tunani, kowa yayima kansa tunani akan al'amarin hakki da yan'ci da matsayin Jagora a wajensa. Gaskiyar magana akan al'amarin Sheikh Zakzaky yawuce ace sai nayi sannan za kayi, ko kuma sai yayi sannan zanyi, ko sai sunyi zamuyi. Ba fa haka bane, kada muyi danasani bayan wasu sun bayarda tasu gudumuwar, MU babu tamu ciki.
Birni da kauye duk inda yan'uwa muke mu kwaci yan'cinmu akan al'amarin hakkin Jagoranmu da abinda idan Jagora yaji ko yagani ko yadawo cikinmu, zaiyi murna da farinciki yace mana Allah yayi mana Albarka, yaji dadi kuma ya gode, kamar yadda tafaru a baya.
Gaskiyar magana wannan lokacin yan'uwa daidai gorgodo anbayarda gudumuwa, Allah yasa harzuwa karshen wannan zaluncin haka za'a cigaba. Ga yan'uwa na wasu wurare da suka san ambarsu a baya wajen wannan al'amarin, yanada kyau suyi karatun tanatsu. Kowa yayima kansa kiyamul layli, Ni dai nasan ban kai yadda yakamata ba kuma na dauki gazawata, Kai da Ke da Mu, duk inda muka gaza mu gyara kuma mu yarda mun gaza. Allah (T) yayi mana taimako, ya amfanar damu.
Daga:M.N.N UPDATES
Tareda wakilinmu:Jibril Usman Sarki

Tags:
Tunatarwa