SAHABBAN ANNABI BASUKAI YAWAN MUSULMIN NIGERIA BA AMMAN SUNYIMA FAJIRAN SHUWAGABANI TAWAYE!!!!

Kayi share domin wasu sugani su Amfana. 


Daga: shafin ma'asumiya Nigeria news updates.


Tareda: Jibril Usman Sarki


Sahabban Annabi ba su kai yawan Musulmin Nijeriya ba, amma ba su yarda sun bi wani tsari ko fajiran shugabanni ba, Sun musu tawaye ne aka yi ta yakar su suna jurewa har sai da suka kafa Musulunci.

Me yasa ba za mu yi koyi da su ba? Me yasa kuke tunanin mafitar mu a katin zabe?

Ba mu dauki darasi ba, cewa duk wanda muke tunanin maceci ne Sai bayan mun zabe shi Sai mu ga ashe macuci ne?

Allah Ya haramta goyon bayan azzalumi da zalunci ko daidai da kwayar zarra ne, inka zabi  wani ya hau mulkin da zai zaluncin raunana ko a shekarar da jinane a karkashinsa baka san kana da kamasho a Lahira ba?

Mu ce Musulunci za mu yi, Malamai ne za su jagorance mu, Alkur'ani ne muke so ya zama shari'ar mu, Musulunci muke so ya zama tsarin mu. Tabbas nan alkairin Duniya da Lahira yake.

Mudake mujure duk wata azaba da muzgunawa harsai munsamun akan acikin dokokin Allah koda kuwa mafiyawanmu zasu kare, munsan cewa basuje abanzaba kuma zasutafi ne amastayin shahidai.

Kamar yadda sahabban manzon Allah (s a w w) suka jure duk wata musiba da hartakaiga sukayi hijra, suka rabu dakomai nasu sukazabi addini yazama mai hukunchi tsakaninsu, har Allah ta'ala yabasu nasara, muma irin abinda yakamata muyi kenan har sai Allah yabamu nasara.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post