SIYASAR KANO TA DAUKI SABON ZAFI 🔥 | BARAU JIBRIN YA JA KUNNEN GWAMNA ABBA KABIR



Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya fito fili ya mayar da martani mai zafi ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan zargin da gwamnatin jihar ke yi masa.


A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Barau ya shawarci Gwamna Abba da ya daina kokarin siyasantar da matsalar tsaro don rufe gazawarsa, ya kuma ce:


"A maimakon bata lokaci wajen zarge-zarge marasa tushe, ya kamata Gwamna ya mayar da hankalinsa wajen magance tarin matsalolin da suka addabi Jihar Kano a karkashin mulkinsa."


Me ya jawo wannan martanin?


Wannan martani na Sanata Barau na zuwa ne bayan da Gwamnatin Jihar Kano, ta bakin mataimakin gwamna, ta zargi Sanata Barau da wasu 'yan siyasa da hannu wajen haddasa rashin tsaro a wasu kananan hukumomi 13 na jihar.


Sanata Barau ya musanta wannan zargi gaba daya, inda ya bayyana shi a matsayin "kage marar tushe" da kuma yunkurin dauke hankalin al'ummar Kano daga ainihin matsalolin da suke fuskanta.


Wannan lamari ya kara nuna irin zaman 'doya da manja' da ake yi a fagen siyasar Jihar Kano a halin yanzu.


Mecece ra'ayinku kan wannan takun-saka tsakanin manyan 'yan siyasar na Kano? Shin zargin Gwamnatin Kano na da tushe, ko kuwa martanin Sanata Barau ya gamsar da ku

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post