Dakarun tsaro sun yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda hudu tare da kama wani jami’in ‘yan sanda da ake zargin yana aiki tare da ‘yan ta’adda a Jihar Taraba.
Wannan lamari ya sake tabbatar da yadda ta’addanci ya zama kasuwanci mai hatsari a ƙasar nan. A baya an kama wani limamin Katolika a Jihar Filato da ake zargin yana safarar makamai, yanzu kuma jami’in tsaro ya shiga hannu saboda haɗin gwiwa da ‘yan ta’adda.
Al’umma sun yi kira da a daina ɗora laifin wasu tsiraru akan gaba ɗaya kabilu. Kamar yadda ake samun marasa kyau a cikin Fulani, haka ake samu a cikin sauran kabilu: Ibo, Yarbawa, Tiv, Berom, Kanuri, Itsekiri da sauransu.
Lokaci ya yi da za a daina zargin al’umma gaba ɗaya, a maida hankali wajen hukunta mutum ɗaya bisa laifinsa, ba tare da la’akari da asalinsa ba.
Addu’a ta ci gaba da kasancewa cewa Allah Ya ci gaba da tona asirin masu aikata laifi da masu goyon bayansu, Ya bayyana dukkan shirin su, Ya kuma kawo ayyukansu fili.
#Tsaro


