DA A ƘARA JAHOHI 5 A NAJERIYA, GARA A YI AMFANI DA WAƊANNAN MAƘUDAN KUƊAƊE WAJEN MAGANCE MANA MATSALAR TSARO A MANYAN JAHOHI 5 DA SUKA FI FUSKANTAR BARAZANA A AREWACIN ƘASAR NAN."

 


TSAKANIN ƘIRƘIRAR SABBIN JIHOHI 5 DA KUMA CETON RAYUKAN AL'UMMAR JIHOHI 5: WANE NE YA FI MUHIMMANCI?


Don Allah Dan uwana Talakkan Nigeria Daure Ka karanta Wannan Sakon Kuma Katayani Isar Dashi...! 


A yau na tashi da wani labari mai kama da almara, amma kuma ana yaɗa shi a matsayin gaskiya, Ban Gasgata ba Sai Danaga Manyan Jaridun kasar nan sun Kawo shi. labarin shirin ƙara wasu sababbin jahohi guda biyar a ƙasar nan, Najeriya. A ƙasar da muka daɗe da sallamawa wutar lantarki NEPA, muka rungumi hasken rana (Solar) a matsayin mafita. A ƙasar da ruwan famfo ya zama abin kallo a gidan tarihi. A ƙasar da ilimi ke neman durƙushewa, kuma matasa masu digiri ke yawo a titi ba tare da aikin yi ba.


Mafi muni kuma mafi tayar da hankali, a ƙasar da ake yanka mutane kamar dabbobi a kullum a yankin Arewa, inda kauyuka suka zama kufai, kuma manoma suka bar gonakansu saboda tsoron 'yan bindiga. A daidai wannan lokaci da muke cikin wannan hali na rashin tabbas da juyayi, wai yau batun da ya fi muhimmanci a gaban wasu shi ne na ƙirƙirar sababbin jahohi!


Abun tambaya a nan shi ne: Wace irin jiha ce za a ƙirƙira a cikin ƙasar da babu kwanciyar hankali? Shin ofisoshin sabbin gwamnoni da 'yan majalisu za a gina a inda ake garkuwa da mutane a kan titi da rana tsaka?


Gaskiyar magana ita ce, wannan shiri, idan har gaskiya ne, tamkar cin fuska ne ga dimbin al'ummar da ke cikin mawuyacin hali. Kuɗaɗen da za a narkar wajen gina sabbin ofisoshi, sabbin gidajen gwamnati, biyan sabbin gwamnoni da 'yan majalisu... wannan kuɗin, a zahirin gaskiya, kuɗin jininmu ne! Jinin waɗanda ake kashewa a kullum ba tare da an ɗauki mataki ba.


Don haka, ina son in miƙa shawara da kuma kira ga hankali da murya mai ƙarfi:


"DA A ƘARA JAHOHI 5 A NAJERIYA, GARA A YI AMFANI DA WAƊANNAN MAƘUDAN KUƊAƊE WAJEN MAGANCE MANA MATSALAR TSARO A MANYAN JAHOHI 5 DA SUKA FI FUSKANTAR BARAZANA A AREWACIN ƘASAR NAN."


Waɗannan jahohin su ne ginshiƙan da idan suka gyaru, zaman lafiya zai samu gindin zama a Arewa baki ɗaya:


Jihar Zamfara: Wacce ta zama tamkar fagen daga, inda rayuwar ɗan adam ba ta da wani daraja a idon 'yan ta'adda.

Jihar Sokoto: Inda hare-haren kan iyakoki da sace-sacen mutane ya hana mazauna barci.

Jihar Katsina: Gidan Tsohon Shugaban ƙasa, amma kuma ta zama gidan tsoro ga mazaunanta.

Jihar Kaduna: Inda hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama tarko, kuma kauyukan kudancinta anas sha jini.

Jihar Neja: Wacce take da faɗin ƙasa amma ta zama mafakar 'yan ta'adda, suna karɓar haraji daga mutane.

Shin ofishin sabon gwamna ya fi rayuwar ɗan talakan da ake yanka wa a gona daraja? Shin sabuwar kujerar sanata ta fi muhimmanci a kan tsaron lafiyar matafiya?


Ya ku shugabanni, ku sani cewa fifita buƙatun siyasa fiye da rayuwar al'umma babban cin amana ne wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba. Mu a matsayinmu na al'umma, muryarmu ɗaya ce:


RAYUWARMU TA FI SABUWAR JIHA MUHIMMANCI!


Ku wadata sojoji da kayan aiki, ku samar da dabaru na zamani, ku magance talauci da rashin aikin yi da ke haddasa shigar matasa wannan harka. Wannan shi ne abin da muke buƙata, ba sababbin sunayen jahohi a cikin taswirar ƙasar da ke cikin haɗari ba.


Allah Ya kawo mana mafita, Ya kare mu daga sharrin mahassada da azzalumai.


Daga naku,

( Mas'udu Dan Masani Shinkafi ✍️ )

Marubuci mai zaman kansa.


Kuma shugaban Shafin Ma'asumah Nigeria News Update 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post