An dakatar da shafukan fitaccen mawakin nan na Najeriya kuma mai fafutuka, Eedris Abdulkareem, a kan manhajojin Facebook da Instagram, mallakar kamfanin Meta.




An dakatar da shafukan fitaccen mawakin nan na Najeriya kuma mai fafutuka, Eedris Abdulkareem, a kan manhajojin Facebook da Instagram, mallakar kamfanin Meta.


Wannan mataki mai cike da cece-kuce na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Eedris ya fitar da wata sabuwar waka mai taken "Wasiƙa a Buɗe zuwa ga Donald Trump," inda ya caccaki tsohon shugaban na Amurka.


Eedris Abdulkareem, wanda ya shahara da waƙarsa ta "Nigeria Jaga Jaga," ya daɗe yana amfani da waƙoƙinsa wajen sukar gwamnatoci da nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al'amura a duniya.


Wannan ya janyo wata babbar muhawara:


Shin Meta (Facebook) sun dakatar da shi ne saboda sukar da ya yi wa Donald Trump, wanda hakan zai zama danne 'yancin faɗar albarkacin baki?

Ko kuwa akwai wasu kalamai a cikin waƙar ko a shafinsa da suka saɓa wa dokokin amfani da manhajojin nasu?

Wannan lamari ya sake nuna irin katon ikon da manyan kamfanonin fasaha suke da shi na tantance abin da za a faɗa da wanda ba za a faɗa ba a shafukansu, wanda hakan ke tasiri kai tsaye a kan 'yancin jama'a a fadin duniya.


Mecece ra'ayinku kan wannan batu?


Shin kun goyi bayan wannan mataki na Facebook?

Ko kuna ganin an danne wa Eedris 'yanci ne saboda ya faɗi ra'ayinsa?

#MaasumahGarkuwarGaskiya #EedrisAbdulkareem #Facebook #Instagram #Censorship #YancinFadarAlbarkacinBaki #Trump #Meta #Najeriya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post