YAN GWAGWARMAYAR IRAQI SUN KAI HARE-HARE CIKIN KASAR TATSUNIYA,

 


Dakaru masu gwagwarmaya a cikin kawancin Mukawama a kasar Iraki sun kai farmaki da makaman jirage masu kunan bakin wake kan birnin Hasfa nab akin tekun Medeteranina a cikin HKI.


Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto wata  majiyar tsaro na kasar Iraki na bada labarin cewa dakarun Mukawama sun cilla makamai na jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa kuma masu konar bakin waje kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Haifa na kasar Falasdinu da aka mamaye.


A ranar jumma’an da ta gabata ce shugaban kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar ta Iraki Abu Ala-alwalaee, ya bayyana cewa dakarun mukawama a kasar Iraki sun shiga wata sabuwar marhala a gwagwarmayanta da HKI don tallafawa Falasdinawa a Gaza.


Al-alaaee ya bayyana cewa nan ba dadewa ba za’a ga sauyi a cikin yakin da dakarun mukawama na kasar Iraki suke yi da HKI.


Wasu kafafen yada labaran sun bayyana cewa a cikin  sa’o’ii 24 da suka gabata sojojin HKI sun  kashe falasdinawa akalla 71 a gaza a yayinda wasu 182 suka ji rauni.


Wannan ya kawo adadin Falasdinawan da suka yi shahada tun ranar 7 ga watan Octoban day a gabata zuwa 36.550, a yayinda wadanda suka ji rauni kuma suka kai 82,959.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post