KASAR TATSUNIYA TAI MAMAKI HIZBULLAH TA SAMI MAKAMI SAMFURIN ‘AlMAS’

 



Hare haren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta rikita al-amura da dama a cikin HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jiridar ‘Foreingn policy’ ta kasar Amurka, daga bakin shugaban cibiyar Almo ta HKI Sarit Zehavi yana bayyana tsaronsa da yadda sojojin kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon suke sami makami mai linzami samfurin Almi mai wargaza tankunan yaki.


Zehavi ya kara da cewa mun san kungiyar tana da fasahar, amma bamu san cewa ta mallaki makamin ba, sai bayan ta yi amfani da shi har sau biyu a kan cibiyoyin tsaro da sojen HK a cikin makonnin da suka gabata.


Zehavi ya ce: A yanzun bamu san yadda zamu fitowa wannan lamarin ba, don tukkan tankunan yakin HK suna cikin hatsari.


Mayakan Hizbullah sun kai hare hare har gudabiyu a makon da ya gabata kan cibiyar Sky Dew na HKI tare da amfani da makamin linzami samfurin S-5 wanda kuma ta cilla shi daga jirgin saman da ake sarrafashi daga nesa. Makami ya sami cibiyar liken asiri mafi girma a yankin arewacin HKI IOF. Sannan ta amfani da makamin kan wata tankan a HKI ya kuma wargazashi.


Ana zaton kungiyar ta sami wadannan makamai masu muhimmancin ne daga hannun kasar Iran ko kuma kasar Rasha.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post