AYYUKAN YAUMU 'DAHAWUL ARDI' (Ranar da Allah ya shinfida Kasa).


 


Yau Lahadi 25 ga wata Zul-qa'adah mai albarka,  Wato a irin wannan ranar ne Ranar  Dahwul ardi, ma'ana ranar da Allah (Swt) ya shimfida Kasa ta zauna daram a doron ruwa.


Allah (Swt) yana fada a cikin Littafinsa mai tsarki cewa:


 "وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَا"


"Kuma, ƙasa a bayan haka Ya Shimfida ta". Suratun-Naazi'ati aya ta 30.


An samo daga Imamu Ali ar-Rida (As) ya ce: " Daren 25 ga Zul-qa'adah shine daren da aka haifi Annabi Ibrahim (As) a cikinsa, kuma a daren ne aka haifi annabi Isah (As), kuma cikin sa Allah ya shimfida Kasa daga Karkashin Ka'abah, duk wanda ya azumci ranar kamar ya azumci watanni Sittin ne". Wasa'ilus-Shi'a hadisi na 4499. 


A wata ruwayar ma akwai cewa: "Kuma a cikin sa ne Qa'im (ATF) zai bayyana"


Ya zo a ruwaya cewa:   "Farkon rahamar da ta fara sauka daga sama zuwa Kasa, a cikin Ashirin da biyar ne daga watan Zul-qa'adah, duk wanda ya azumci wannan ranar kuma ya tsayu a cikin daren (Ya raya daren), yana da ladar ibadar Shekaru dari, wadan da ya azumci wuninsu ya kuma raya Dararensu".


 Wasa'ilus-Shi'a juzu'i na 10 Shafi na 451.


WASU DAGA CIKIN AYYUKAN RANAR 'DAHAWUL ARDI':


1. An so a yi wanka a ranar.


2. Ana so a azumci ranar. Ranar tana daga cikin raneku 4 na shekara da aka karfafi azumtar su.


3.  Akwai Sallah Raka'a 2 da ake yi da hantsi, kowace Raka'a Fatiha da Was-Shamsi 5, bayan Sallama a ce: LA HAULA WA LA QUWWATA ILLAH ALIYUL AZIM.


4. An so a Ziyararci Imam Ali Ar-ridha (As), An ambata cewa ziyararsa a irin wannan ranar yana daga cikin Ayyukan mustahabi mafi girma.


 Da Fatan Yan Uwa Ba Zamu Manta damu Cikin Addu’o’insu Masu Albarka Ba.


Daga Shafin Sheikh Ahmad Yashi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post