IRAN TANA DA KARFIN SOJA DON HAKA BABU MAI TUNANIN YAKI DA ITA,


Shugaban kasar Iran na riko ya bayyana cewa: Iran a yau tana da karfin soja don haka babu mai tunanin shiga yaki da ita


Shugaban hukumar zartaswa kuma shugaban riko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Mokhber ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau tana da karfi kuma babu mai tunanin kalubalantarta ta hanyar soji, yana mai jaddada cewa gwagwarmayar da al’ummar Gaza ta ke yi a yau a matsayin wani bangare na gudumawar Imam Khumaini {r.a} na fadakar da al’umma kan neman ‘yanci.


Mukaddashin shugaban kasar ta Iran ya gabatar da wannan jawabi ne a yammacin jiya Lahadi aa yayin juyayin cika shekaru talatin da biyar da rasuwa wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci Imam Khumaini {r.a} da zaman juyayin ya samu halartar dimbin iyalan shahidai da malaman addini da kuma bangarori daban-daban na al’umma.


Mukhbar ya kara da cewa: Mafi girman halayen Imam Khumaini shi ne imani da Allah da dogaro da shi, kuma Imam ya kasance mai imani da alkawarin Allah. Sannan duk wani yunkuri da Imam ya yi, ya yi shi ne da a kan tubali na zurfin tunani da hankali.

@Ma'asumah Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post