HUKUNCE-HUKUNCEN MAMACI (GAWA)

1. Wanda ya kai gargara (kusa mutuwa); ana son a kwantar da shi  ta bayansa (ya jingina da wani abu), fuskarsa da kafafunsa suna fuskantar Al-Qibla.
2. Mustahabbi ne a lakana masa Kalmar Shahada, ikirari da Ma'asumai(as) da karanta masa Suratu Yasin da As-Safat.
3. Yayinda mutum ya mutu; mustahabbi ne rufe idonsa, bakinsa, mikar hannayensa, daidaita jikinsa, suturtashi, sanar da rasuwarsa da kunna masa fitila (idan da dare ne).
4. Makaruhi ne barin Mamaci shi kadai (kafin a binne shi).
5. Makaruhi ne mai Janaba ko Haila su halarci wajen Mamaci.
6. Mustahabbi ne karantawa Mamaci Qur'ani da yi masa addu'a.
7. Makaruhi mace ta raka Mamaci (zuwa makabarta) ko barin ta ita kadai gun Mamaci (kafin a binne shi).

WANKAN MAMACI (GAWA)

1. Wajibi ne yiwa Mamaci wanka, Likafani, Sallah da binne shi.
2. Namiji ne zai yiwa namiji wankan gawa, mace ce zata yiwa mace, amma miji zai iya yiwa matarsa, kamar yanda itama mata zata iya yiwa mijinta.

YANDA AKE WANKAN MAMACI (GAWA)

1. Kawar da dukan najasa daga jikin Mamaci
2. Wanke Mamaci da ruwan bagaruwa
3. Wanke Mamaci da ruwan Kafur (ko wani turaren)
4. Wanke Mamaci da ruwa zalla
5. Idan babu Bagaruwa da Kafur; za'a yiwa Mamaci wankan duka uku (3) da ruwa zalla.
6. Farawa da wanke kai zuwa karshen wuya, sannan tsagin jiki na dama, sannan na hagu.

LIKAFANI

1. Gyauto: kyallen da zai suturce cibiya zuwa gwiwa.
2. Riga: kyallen da zai rufe kafaɗa zuwa kwari
3. Mayafi: kyallen da zai rufe dukkan jiki.
4. Wajibi ne likafini ya kasance mai tsarki, halastacce, kar ya zama zallar Al-harini ko fatar dabbar da ba'a ci.

SAKAWA MAMACI TURARE

1. Wajibi ne sakawa Mamaci turare; kafin ko bayan Likafani.
2. Wajibi ne turaren ya kasance Kafur. A shafawa Mamaci a gabobin Sujadah; ya fito sosai. Mustahabbi ne a surka da Turbatul-Husainiyyah.

SALLAR MAMACI (GAWA)

Wajibi ne yiwa Mamaci Sallah; bayan yi masa wanka da Likafani, kafin a binne shi.

YANDA AKE SALLAR MAMACI (GAWA)

1. Kabbara da yin Kalmar Shahada
2. Kabbara da yin Salatin Annabi(saw)
3. Kabbara da yin addu'a ga Muminai
4. Kabbara da yiwa Mamaci addu'a
5. Kabbarar karshe (ita ce sallamewa).
6. Mustahabbi ne yin jam'i a sallar Mamaci
7. Akwai addu'o'i mustahabbai da ake son karantawa a sallar Mamaci; za'a iya samun su a littattafan addu'o'i (Mafatihul-jinan...).

SHARUƊƊAN SALLAR MAMACI (GAWA)

1. Yin Niyyah (neman kusanci da Allah)
2. Ayyana Mamaci
3. Fuskantar Al-Qiblah
4. Tsayuwa
5. Kan Mamaci ya kasance a damar masu sallar
6. Kar a samu shamaki tsakani gawar Mamaci da masu sallar
7. A samu daidaitar mahallin yin Sallar.

BINNE MAMACI (GAWA)

Wajibi ne binne Mamaci, a kwance ta gefen damarsa. Fuskarsa, cikinsa da kirjinsa suna kallon Al-Qiblah.

WANKAN TABA MAMACI

Wajibi ne yin wankan tsarki ga duk wanda ya taba Mamaci kafin a yi masa wanka, sai dai in mamacin Shahidi ne. Taba Mamaci yana warware Al-wala. Wankan taba Mamaci baya dauke Al-wala.

HALAS NE YIWA MAMACI KUKA, SAI DAI BAI HALAS YIN KURUWA (IHU), TSAGA JIKI...

HARAMUN NE TONE KABARIN MAMACI; SAI DAI IDAN:

1. An binne shi a gurin da bai halasta ba
2. Ana son a yi wani bincike don tabbar da wani hakkin
3. Idan ba'a yi masa wanka ko Likafani ba
4. Ana son canza masa kabarin da ya dace da shi.
5. Ana tsaron maƙiyi ko dabbobi zasu lalata gawarsa.

MARAJI'U (REFERENCES)

- منتخب الأحكام (طبقا لفتوى آية الله الخامنئي)، الشيخ حسن العاملي، دار الولاية، بيروت لبنان. 2012

- زبدة الأحكام، طبقا لفتوى آية الله الخميني، طهران إيران، 1404 ه‍

- أجوبة الاستفتاءات، السيد علي الخامنئي، ...

- توضيح المسائل، السيد السيستاني، الطبعة : الرابعة. تاريخ النشر : ١٤١٥


Sani Muh'd Sani Muh'd
Baban humaid Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post