ANGABATAR DA WALIMA TARE DA MAULUDIN IMAM MAHDI (AJF) DANA JAGORA (H) A DA'IRAR KAZAURE

 


A yau Lahadi 15 ga watan sha'aban 'yan uwa Almajiran Sayyeed Zakazaky (H) suka gabatar da walimar dawowar jagora daga neman Lafiya tare da Mauludin Imam Mahdi (Ajf) da kuma na jagora (H) shidai wannan program an gabatar dashi ne a muhallin 'yan uwa na Da'irar kazau da yammacin yau. Inda aka fara Bude taro da Addu'a tare da karatun AlQu'ani sai kuma aka gabatar da shu'ara suka gwangwaje wajan da yabon Imam Mahdi tare da jagora.


Bayan kammala wadannan abubuwa sai aka gabatar da hujjatul Islam walmusl Sheik Magaji Mai wada wanda shine ya gabatar da dan takaitaccan jawabi akan lmamul hujja ATF da jagora bayan kammala jawabin ne se aka gabatar da 'Yan tamsiliya inda Suka maida hankali akan halin rayuwar da muka tsinci kammu aciki sannan sai aka gabatar da walima. Akayi Addu'a aka salami kowa


By Real Naseer Ma'asumah Ng ✍️

15/8/1445 25/2/2024

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post