TSARABAR MAULIDIN GARIN NINGI !!!

 
SAI KA SAN WANENE ANNABI (S. A. W. W) SANNAN ZA KA SO SHI


A jiya asabar 16th December, 2023 ne 'yan'uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Da'irar Ningi dake Jihar Bauchi su kayi Maulidin Khatama.


Sheikh Tahir Umar Sulaiman Bauchi ne  babban baqo  wanda ya shayar da mahalarta da gwalagwalan jawabai masu kama qwaqwalwa. 


Bayan bude taro da addu'a da kuma sauraron karatun Al-Qur'ani mai tsarki sai aka bawa mawaqa (Sha'irai) fili suka nuna farin cikinsu ta hanyar amfanin da fasaharsu suka yabi Manzon Allah (S. A. W. W) da Iyalan gidansa (A. S). Malam Abdullahi 'Dan Lushi Bauchi shine baqon sha'irin da ya albarkaci fili. 


Bayan mawaqa sun sauka sai kuma 'yan Kareti da Fareti suka qara haskaka filin tare da janyo hankulan masu sauraro da kallo. 


Bayan kowa ya nishadantu sai aka gabatar da babban baqo mai jawabi domin bada abincin ruhi da kuma ilimantarwa. 


Ya fara da nuna godiya ga Allah da yabonSa da kuma salati ga Annabi (S. A. W. W) da iyalan gidansa tsarkaka (A. S), sai kuma ya zarce cikin bayani kan wanda aka taru dominsa. 


Cikin abu na farko da ya fara ambata shine babu ace kaso Annabi (S. A. W. W) ba tare da ka san shi ba. Har ya bada misali da masu ganinsa (S. A. W. W) a matsayin mai yin fitsari a tsaye kan Bola wanda mahaifanta ke cikin wuta.


Yace masu yi masa irin wannan kallo ba su san wanene Annabi ba kuma basu san matsayinsa ba ballantana ace su taru don nuna murnarsu kan samuwarsa. 


Shehin malamin ya bayyana mana matsayin Annabi (S. A. W. W) a matsayin mai kyawawan dabi'u wanda Allah ya yabe su cikin Qur'ani, kuma wanda ya fito daga cikin tsatso na masu sujadah. 


Da yake tabbatar da matsayin mahaifan Manzo cewa akan addinin Annabi Ibrahim suke sai ya bada misali da yadda kafiran wancan zamani suke sanya sunayensu mai nasaba da bauta ga ababen bautarsu na lokaci. Misalin nasu shine :


Abdul-Uzzah, Abdul-Shams, da sauran su. Sai yace amma kakan Manzon Allah (S. A. W. W) da ya tashi sanyawa mahaifin fiyayyen halitta suna sai ya kira shi da Abdul-Lahi, wanda Allah na nufin abin bauta ne qwara daya (1), domin su ababen bauta ana kiransu ne Arbaab.


Shehin yayi kira ga malamai masu cewa wanda ya mutu kan wannan hanya ba Shahidi bane, lalle hakan jahili, domin da Sahabbai suka tambayi Manzon Allah (S. A. W. W) cewa wanene Shahidi, da ya tashi basu amsa ya jero musu sunayensu ciki yake cewa wanda ya mutu a hanyar Allah da wanda aka kashe shi a hanyar Allah.


A qarshe yayi gargadi da a tashi a nemi ilimi na haqiqa wanda za asan Allah da haqqoqinSa da kuma sanin ma'anar tawilin ayoyinSa don a nisanci fassara su da wata fuska wacce ba ita ce ma'anarta ba. Ya kuma ce sanin haqiqanin ilimi fassara ayoyin Qur'ani dole sai an kuma cikin Fassarar da aka samo daga iyalan gidan Manzon Allah (S. A. W. W), domin sune aka bar mana a matsayin abin riqo tare da Al'Qur'ani bayan Manzon Allah (S. A. W. W) masu bayyanar mana Ilimin da ya shige mana duhu. 


Yace abinda Annabi (S. A. W. W) ke nufi da cewa mu lura da abincin da muke ci ba wai ana nufin abincin da ake sanyawa a baki bane, a'a, Ilimin da ake shayar damu ne don kada a shayar da mutum Gubar da za ta nisantar shi da Allah da ManzonSa (S. A. W. W). 

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


            (08137925034)


17th December, 2023/  4th Jimada-Sani, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post