CIKAKKEN BINCIKE KAN MUTUMIN DA WATA MATA TA KASHE A BIRNIN KANO MAI SUNA NAFI'U.

 

Marigayi Nafi'u kenan da Hafsat budurwar sa wadda ta kashe shi

NAFI'U SAURAYIN HAFSAT NE:   Ga yadda bincike ya tabbatar min kan labarin Nafi'u da Hafsat...


Nafi'u saurayin Hafsat ne da jumawa bayan Hafsat tayi aure shine suka ha'da Kai suka fara kasuwanci (Business) tare da Nafi'u Kuma Allah ya basu sa'a suka samu ku'di masu yawa har ita Hafsa ta bu'de Shago a zoo road, Hafsat da mijinta Dayyabu suna zama a wani karamin gida sai Allah ya bu'dewa mijin ya samu ya Gina Babban gida kafin domin su koma can da zama tare da matarsa, kafin nan ita Hafsat ta Riga ta ha'da mijin nata da Nafi'u sun saba harya zama kamar dan Uwa suna harkoki tare ba tare da mijin yasan abinda dake tsakanin matarsa da Nafi'u ba.

Hafsat da mijinta Dayyabu


A lokacin da su Hafsat  za su tare a sabon gidan su shine tace dole sai dai a koma Sabon gidan tare da Nafi'u haka Kuma akayi dole mijin ya amince ance Yana tsoronta kasancewar ta fishi ku'di. 


         Download Fadakdata Application


Ana haka ne Nafi'u bashi da lafiya Kuma Already ya Fa'dawa Iyayensa cewa Yana da Ubangida a Kano ko da Iyayen Nafi'u suka zo Kano  daga bauchi sai Nafi'un ya gabatar da Iyayen nasa ga Dayyabu mijin Hafsat amatsayin maigidan sa ne na kasuwanci, ba kowa yasan cewa Nafi'u saurayin Hafsat bane sai abokan Nafi'un da Kawayenta na kusa, ana zargin Yaron da Hafsat ta Haifa Dan Nafi'u ne domin suna kama sossai.


Ance ko Ina Hafsat za ta tafi tare suke tafiya da Nafi'u har Umrah Kuma mijin Yana kallo ba tare da yace komai ba.Dalilin wannan rigima da ya sa Hafsat ta Kai kashe Nafi'u   shine Nafi'un ne ya Fa'dawa Hafsat cewa zai yi aure ya samu wata matar aure tun lokacin shine ba a sake zaman lafiya ba tsakanin Hafsat da Nafi'u.


Allah ne ya taimakawa mijin Tabbas da shine zai kasance Gawa bisa wannan Dalilin soyayya Dake tsakanin Nafi'u da Hafsat Yanzu dai Hafsat ta kashe Nafi'u, Allah ya jikansa da rahama, jama'a don Allah a kiyaye dokar Allah a zaman aure idan ba haka Bala'i zai Cigaba da faruwa tsakanin Al'ummarmu.


An turamin Hotunan yaron Amma ba zan iya sakawa ba..

Credit M Inuwa.Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post