ABUBUWA SHIDA (6) DA SUKA AUKU A WATAN JIMADA-SANI !!!

 

 

SHAHADAR SHUGABAR MATAN TALIKAI SAYYIDAH FATIMAH (S. A) 


Watan Jimada-Sani wata ne wanda ya tattaro waqi'o'i masu yawa cikinsa wadanda ya kamata a rana kowanne daga cikinsu. 'Daya (1) ne kadai daga abubuwan da suka faru za muce rana ce ta farin ciki, amma duk sauran ranaku ne na jimami da baqin ciki.


(1)- RANAR 3 GA WATA :- Wannan ita ce ranar shahadar shugabar Talikai Nana Fatimah (S. A) wacce tayi shahada cikin shekara ta 11 bayan Hijra. 


(2)- RANAR 10 GA WATA :- Cikin wannan rana ce akayi yaqin Mu'uta da kuma shahadar Ja'afarud-'Dayyar Bn Abu 'Dalib (A. S) cikin shekara ta 8 bayan Hijra. (3)- RANAR 13 GA WATA :- Ita ce ranar wafatin Ummu-Banin Ummu Abbas da 'yan'uwansa cikin shekara ta 64 Bayan Hijra. 


(4)- RANAR 15 GA WATA :- Ita ce ranar shahadar Muhammad Bn Abubakar Bn Abiy Quhafata, cikin shekara ta 38 Bayan Hijra. 


(5)- RANAR 20 GA WATA :- Ranar haihuwar shugabar matan Talikai Sayyidah Fatimah Az-Zahrah (S. A) cikin shekara ta 8 kafin Hijra. 


(6)- RANAR 27 GA WATA :- Ita ce ranar shahadar Imam Aliyu Al-Haadiy Bn Muhammad Jawwad (A. S) cikin shekara ta 254 Bayan Hijra.Wadannan sune abubuwan da suka faru cikin watan, da fatan za a kiyaye lissafi don a raya su.

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


             (08137925034)


15th December, 2023/  3rd Jimada-Sani, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post