*YAN* *UWAN* *MUSULMAI* *ALMAJIRAN* *SAYYID* *IBRAHEEM* *ZAKZAKY* *NA* *GARIN* *AZARE* *SUN* *KAI* *ZIYARAR* *HAPPY* *KIRSMET* *COCIN*

 *YAN* *UWAN* *MUSULMAI* *ALMAJIRAN* *SAYYID* *IBRAHEEM* *ZAKZAKY* *NA* *GARIN* *AZARE* *SUN* *KAI* *ZIYARAR* *HAPPY* *KIRSMET* *COCIN* Yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky na garin Azare sun ziyarci Cocin guda biyu ne Daya tana kan titi Asibiti Ali kaura Dake Nan cikin garin azare, sai Kuma da biyu da take cikin police barek.


A yau Litinin 25/12/2023 ne wasu ba'adin 'yan uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky na garin Azare suka kai ziyarar domin taya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isah almasihu ga 'yan uwan mu a halitta da zaman takewa ta hadamu 


Ziyararce aka shiryata domin wanzar da zumunci da Karin fahimtar juna da cin gaba da kiyayya tsakanin musulmi da kirista.


Malam Auwal masana ya gabatar da takaitaccen jawabi a wurin, inda yake bayyana cewa a lokacin manzon Allah (S) ya zauna da kiristotic lafiya,

 Sai Kuma M Abdurrazaq Dan Katsina ya gabata da wake na tayansu murna.

  Har wani posto ya gabatar da takaicecen jawabinsa har yake gara Jan hankali Yan uwa da sun gujin rudun siyasa,

Ya Kuma Kara da cewa wajibi mu hada kai domin samarwa da kanmu mafita, ta yadda zamu rayuwa cikin salama ba tare da fadan kabilanci.


Daga karshe posto da ma kirstotic Dake cikin cocin sun yaba da irin yadda 'yan uwa musulmin suka tuna dasu har suka ziyarce su. Yace kuma wannan aiki ne Mai kyau da Allah yake so tare da fatan Allah ya kara hada kanmu da fatan zaman lafiya a kasarmu Baki Daya.


Daga karshe akayi addu'o'i akayi hotuna aka rabu cikin girmamawa  


 *MEDIA* *FORUM* *AZARE* 

25/12/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post