ZANGO NA BIYU A YAU ASABAR: Mu'utamar Amm Ya Na Cigaba Da Gudana A Garin Lafiya.

 


A cigaba da babban taron Mu'utamar na ƙasa da ƙasa wanda Almajiran Sheikh Ibaraheem Zakzaky (H) suka shirya kuma yake gudana a garin Lafia Jihar Nasarawa, a yanzu an shiga Zango na biyu a wannan rana ta Asabar 18 ga watan Nuwamba 2023/1445h.


Malam Auwal Gangare Jos, shine ya gabatar da malami mai jawabi Sheikh Muhammad Abbare Gombe wanda yayi jawabinsa akan "Waki'ar NBormi Da Kuma Bukatuwa Zuwa Ga Gwagwarmayar Tabbatar Addini A Wannan Lokaci. 


Sheikh Muhammad Abbare cikin jawabinsa, ya fara ne da batun zuwan Turawa Nigeriya, yadda suka ɗauki mutane da sunan aiki suka mayar dasu. (Bayi) kayan aikin su. 


Bayan Shehun Malami ya bada dogon tarihi akan Sarki Umar na Gombe da irin mummunar dabi'unsa, daga karshe yace wannan Sarki Umar shine silan da ya jagoranci turawa suka yaƙi Sidi Attahiru Bormi a garin Bajoga. Kafin wakiyar Bormi, Sidi Attahiru ya tara al'ummar Musulmai na wannan lokaci cikin masallaci ya musu Khudba da cewa, "Kowa ya shiryawa mutuwa, domin gobe insha Allah muna aljanna" a washe gari kuwa turawan mulkin mallaka suka dira akan al'ummar wanda suka musu kisan da duk nahiyar Afirka ba'a taba yin irin wannan mummunar kisan ba. Daga karshe jawabin Sheikh Muhammad Abbare ya karkare da cewa, yanzu duk abin da suka yi a Bormi ya hana mutane addini ne, duk da sanin tarihin abin da ya faru mun yi imani da addinin nan sai ya tabbata ƙarƙashin "La'ila-Ha-illallah Muhammad Rasulallah"


#LafiaConference2023

#MuutamarLafia2023

#FreePalastine 

18/ November 2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post