CIKAKKEN ROTON MUZAHARAR MAULUDIN MANZON (ASWW) A DA,IRAR RONI.

 CIKAKKEN ROTON MUZAHARAR MAULUDIN  MANZON (ASWW) A DA,IRAR RONI.Rabiu Badamasi


Yan uwa musulimi Almajiran sayyid zakzaky(H) Na da,irar roni da kewaye sun gudanar da gagarumar  muzaharar Maudun Manzon Allah (Asww).


Da safiyar yau Asabar ne aka gudanar na Muzaharar An dagota ne misalin karfe 11:30pm na Safiyar yau An dago Muzaharar ne daga inda aka saba dogota wato Masallacin idi dake Cikin garin Roni aka taho ta ita aka biyo ta kantauni ana tagfiya cikin tsari anshiga ta unguwan islamiyya (wajan ma,aka) aka shigo ta kofar gari sanna aka biyu ta cediya muka shiga ta makauraci sanna aka biyo ta kasuwar ciki muka biyo ta kwatsatsa sai aka biyo ta kanti.


Muna tafiya ana rera yabon ma aiki (saww) Wanda a gefe guda kuma ga yan fareti suna taka faretin Girmamawa ga manzon Allah (saww) sanna aka biyo da Muzaharar ta tudun Dan biri-biri sanna muka shgo ta tashar kado sai muka shiga ta sabuwar unguwa sanna aka shigo ta tsallaken kwalta.


Gefe guda gamalamikiu yan Albarka nan suma duk a sahun Muzaharar duk sun fitone domin murna haihuwar Annabin rahama daga tsallaken kwalta muka shigo ta kan wahawa da nan sai aka biyo ta tashar ido sanna muka shiga ta rahamawa sai gamu a bakin makaranta inda nan ne masallacin juma,a yake Wanda anan ne za,a sauke Muzaharar inda zakuga yan uwa sisters suma a sahun Muzahara ga yan uwa Hurras suma a cikin Muzahara.


Lokacin da,aka karaso masalla cin juma,a lokacin sallar azuhur yayi wanna yasa ba,a zamu damar taka fareti ba kawai an gudanar da jawabi ne Wanda malam Abubakar wakilin yan uwa na garin ingawa yayi jabi akan yadda manzon Allah ya tafiyar da rayuwar Sa sanna yayi mana Jan hankali aka muhimmatar da al,amarin Maulud sanna malm Abdussalam Abubakar ya Dan gajeren jawabi sanna akayi Addu,a aka sallami Taro.

#MUHAMMADURRASULLUH.


Rabiu Badamasi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post