ABUBUWANDA SUKE SAUƘAƘA WA MUTUM MAGAGI DA RADADIN MUTUWA

 


1-} An ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) yace:  “duk wanda yake son Allah ta'ala ya sauƙaƙa masa magagin mutuwa, to Allah zai sauƙaƙa masa kuma ba zai yi talauci ba har abada.”


2-} An ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) yana cewa, “wanda ya tufatar da Dan uwansa tufafi irin na lokacin zafi ko lokacin sanyi.”


Akwai rigar sanyi Wanda ake sanyawa wanda za a ji dadi lokacin sanyi, hakan akwai na zafi wanda ake sanyawa aji dadi lokacin zafi.


Imam yace duk wanda ya tufatar da ɗan uwansa mumini to, haƙƙin Allah ne akan Allah ya sauƙaƙa masa radadi da magagin mutuwa.


3-} Kuma an ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.w) yace: “duk wanda ya ciyar da ɗan uwasa zaƙi wato,  ɗan uwansa yaji ɗadi to shima haka Allah ta'ala zai cire masa daci da radadin mutuwa.


4-} Kaf'amiy ya ruwaito daga Manzon Allah (S) cewa: “wanda ya ke karanta wannan Addu'a a kullum ƙafa goma (10). Allah zai gafartamasa manya manyan zunubansa guda dubu hudu. Kuma Allah zai tseratar da shi daga raɗaɗi da magagin mutuwa, da azaban ƙabari da kuma wahalhalu guda dubu ɗari na ( *ƙiyama* ). Kuma Allah zai kareshi daga sharrin shaidan da rundunarsa. Kuma Allah zai biya bashin da ake binsa,Kuma Allah zai kawar masa da damuwowi da ƙuma ƙunci da yake ciki.”


wannan Addu'ar itace:


 " A'adadti li kulli haula la'ilaha I'll Allah,Wa likulli hammin wa gammi Masha Allah,Wa likulli Ni'imati Alhamdulillah,Wa likulli Raka'i shukran lillah, Wa likulli A'ajubat subhanallah,waikulli zanbin Astagfirullah, Wa likulli ma'asiyatu Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,Wa likulli Daiƙi Hasbiyallah,Wa likulli Qada'i was qadari Tawakkaltu Alallah,Wa likulli Aduwwa I'itisamtu Billah,Wa likulli Da'atu wa ma'asiyatu Lahaula Wala ƙuwwata Illa billahil Aliyul Azeem.


Ya Allah muna roƙonka ka mana tsari da raɗaɗi da magagin mutuwa a ƙarshen rayuwa.


 Khadiminku:  ✍️Muhammad Baqeer Adamu

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post