WASU HADISAN FALALOLIN SAYYIDA ZAHRA {SA} SHUGABAR MATAN DUNIYA DA AL'JANNA...

Ma'asumah Nigerian News Update 

Yazoo cikin littafin Ma'anil Akhbar na Sheikh Sadook: Jildi na 15, Shafi na 64,haka kuma Allama Majlisi ya kawo cikin Biharu Anwar,Jildi na 6, Shafi na 12, cewa:  

An tambayi Imam Jafar Sadik (AS): Me Yasa aka kira (Sayyida Fatima) da'Azzahara'u'? Sai Imam Sadik (AS) Yace: "Saboda ta kasance idan ta tashi Sallah a wajan da take yi,hasken ta na bayyana ga al'ummar sama kamar yadda yadda hasken taurari ke bayyana ga al'ummar duniya." 

Yazoo cikin ittafin Dala'ilu Imama, Shafi na 52: 

Dagaa Zaid bin Musa wanda sanadin sa ya kare akan Imam Ali (S.A) yace: Manzon Allah (S.A) Yace: "Hakika Allah ya halicci Fatima yantatta (mara haidha) da siffar mata,Saboda 'ya'yan Annabawa basu Haila." Abu Muhammad bin Ali Faqihi Ash'shami,Abu Taib bin Ahmad Nasirul Hafiz ya bamu labari, Aliyu bin Sa'id bin Bashir ya bamu labari, daga Abada bin Ya'aqub,Muhammad bin Isma'i bin Raja'a Zabidi ya bamu labari, daga Ishaq Shaibani,daga Jami'i bin Umair, yace: Munje-wajan Aisha nida mahaifiyata, sai yaji ta labule tana tambaya akan Aliyu, Sai Aisha tace:Kina tambayata mutumin da na rantse da Allah bansan wani mutum da Manzon Allah yafi so sama dashi ba, haka kuma babu wata mace a doron kasa da Manzon Allah (S) ke so kamar matar Ali (Fatima). 

Babann Humaid Mnnu//Ng0027 📝

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post