DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A. S) (11)

 


WAWA BAI SAN HAQQIN MAI HAQURI BA

Haquri siffa ce ta Annabawa da Manzanni (A. S), kuma siffa ce ta muminai masu koyi da fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W). 

Babu wani abu da ake cimma masa na alkhairi dole sai da haquri, amma shi wawa bai san matsayin haquri da haqqin mai yinsa ba. 

Ya zo daga kalaman hikima na Imam Ali (A. S)  cewa :

                👇

قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):

" الْحُمْقُ دَاءٌ لَا يُدَاوَى وَمَرَضٌ لَا يَبْرَأُ."

" SHI WAWANCI CUTA CE  WACCE BA A YI MATA MAGANI, KUMA CIWO NE DA BA YA WARKEWA. "

المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم

Idan akayi maganar wawanci anan ba wai ana nufin rashin karatu bane ballantana kace in anyi karatu zai warke. A'a,   ana samu da yawa daga cikin wadanda su kayi karatu wawaye ne. 

Wawa shine wanda ba ya iya ganin gaskiya ballantana ya bi ta, sannan ba ya iya sanin haqqoqi ballantana ya sauke. 

A wani guri Imam (A. S) yace :

قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):

 " لَا يَعْرِفُ السَّفِيهُ حَقَّ الْحَلِيمِ."

" SHI WAWA BAI SAN HAQQIN MAI HAQURI BA. "

المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم

Shi wawa a duk inda yake yana kallon mai haquri a matsayin matsoraci ne ko kuma wanda bai san haqqinsa ba. 

To, kaga kuwa mai irin wannan fahimta ba zai iya sauke haqqin mai haquri ba domin bai san matsayinsa ba. 

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


          (08137925034)

17th November, 2023/ 4th Jimada-Ulah, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post