ME AKE NUFI DA SHI'A?/SU WANE NE YAN SHI'A?Mutane da yawa Suna ma "Shi'a kallon wani Abu daban Kuma, suna Mata mummunan zargi, da Ance wane Dan shi'a ne Shikenan Kamar Ance wane kafiri ne wa'iya zibillah🤦🏻‍♀️🥹.


Kalmar "shi'a" Dai kalmar Larabci ne Wanda take Nufin "Mabiya" ko "Jama'a" A fassara mafi Inganci. A Addinince  Yana Nufin "Magoya Bayan Imam Ali (A.S)" 


SU WANE NE YAN SHI'A?


1__ 'Yan "shi'a" Sune wadanda suka miqa Wilayan su ga Imam Ali (A.S) Sukayi Imani Dashi a Matsayin Wasiyyin Annabi (S) majibincin Lamarin su, Kuma Imami na farko.


2__'Yan shi'a sune wadanda suka yi Ruqo da wasiyan manzon Allah (S) Suka Riqe Al'qurani da Ahlulbaity (A.S)


3__ 'yan shi'a sune Sukayi Imani da Imamai Goma shabiyu 12 A bayan Manzon Allah (S)


4__An Tambayi Manzon Allah (S) su waneye kairul Bariyya? Sai yace " 'HUM ALIYU WA SHI'ATIHI

 (sune Aliyu da Jama'arsa)".


Mu Hadu a Kashi na Gaba insha Allah inda zamuji matsayin Imam

 Ali (A.S) a Addini, matsayin shi a wajen Annabi (S), da karamomin shi.


__Khauthar Muhammad Auwal Aqeelah

✍🏻🌹✍🏻

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post