Yadda Zaman Sasanci Ya kasance a Tsakanin Ƴan Ta'adda Da Jama'ar Gari A Jihar Katsina


 Yadda Zaman Sasanci Ya kasance a Tsakanin Ƴan Ta'adda Da Jama'ar Gari A Jihar Katsina

Daga Muhammad Aminu Kabir 

Lamrin samar da tsaro ya zama abinda ya zama tun ana sace Mutane suna biyan kuɗin fansa har ta kaiga kiran zaman sasanci tsakanin ƴan ta'addar daji da Mutanen gari.

A jiya Asabar 16/09/2023 aka gabatar da zaman sasanci tsakanin ƴan ta'adda da mutanen gari a ƙauyen Fankama dake ƙaramar Hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Kamar dai yadda muka gani a hotuna ga Ɓarayin nan ɗauke da makaman su hadda masu kayan Sojoji babu ko alamar nadama, sai dai abin farin ciki shine anyi zaman sasancin kuma an sami fahimtar juna kuma zaman anyi lafiya an tashi Lafiya.

Allah ya kyauta gaba ya zaunar damu lafiya Amin.

Real Naseer Umar 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post