An haifi Annabi Muhammad (s a w w) 17. Ko 12 Ga wata a'ina sabanin yake?



Ma'asumah Nigerian News Update

A bisa ingantattun ruwayoyi), an haifi Manzon Allah (s) ne a ranar 17 ga watan Rabiul Awwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ran 12 ga wanann wata ne, a garin makka a shekarar da ake kira da Shekarar Giwaye . 


Dalilinda ya sa ake kiran wannan shekara da haka kuwa shi ne wani gwamnan Sarkin Abbasiniya ne mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa Dakin Ka'aba da sauya alkiblar mutane zuwa San'a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka'aba) inda da ma tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. 


Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna tasa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye dauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinka jefo wadannan tsakuwoyi a kan wadannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah Ya yi maganin wannan azzalumi da mutanensa.


Mahaifinsa dai shi ne Abdullah dan Abdul Mutallibi dan hashim; Mahaifiyarsa kuwa ita ce Amina 'yar Wahb Kakansa kuwa shi ne Abdul Mutallibi, wanda ya kasance yana da 'ya'yaye da yawa, amma Abdullahi (mahaifin Annabi) da Abu Talib (mahaifin Imam Ali) mahaifiyarsu guda ne. 


Don haka ya fito ne daga cikin madaukakin gidan nan na Bani Hashim wanda ya fito daga kabilar kuraishawa wadanda ke da dangantaka da Annabi Isma'il (a.s) dan Annabi Ibrahim (a.s). Manzon Allah (s) dai ya tashi ne a matsayin maraya saboda kasancewar mahaifinsa ya rasu yayin da ya kai ziyara Yathrib (Madina) watanni uku kafin haihuwar Manzon Allah (s). Tattare da bakin cikin rasuwar Abdullah, amma haihuwar wannan maraya ta sanya iyalansa, Amina da Abdul Mutallib, cikin farin ciki da ba shi da iyaka. 


Sun shirya gagarumar walima ga 'yan'uwa da makwabta, inda aka yi yanka don murnar wannan haihuwa. A sakamakon haka duk Makka ta dauki murna, inda mutane suka yi ta zuwa gidan Abdul Mutallib don mika sakon taya murna gare shi.


A bisa al'adar mutanen Makka, sukan kai 'ya'yayensu shayawar kauye saboda samun kyawawan dabi'dabi'u da kuma yanayi mai kyau da dai sauransu, don haka an aika da Muhammad (s.a.w.a) wajen da Halima 'yar Abi Zu'aib al-Sa'adiyya a kauye don shayar da shi. 


Hakika Halima ta sadu da alhairai masu yawa daga abin shayarwarta Muhammad (s.a.w.a) Lokacin da al-Mustafa ya cika shekaru shida da haihuwa sai Halima ta dawo da shi zuwa Makka, yayin da ya sami kakansa Abdul-Mudallibi a matsayin mafi alherin mai reno gare shi; domin ya kasance yana ba shi duk abin da yake bukata na tausayi da kauna irin ta iyaye masu lura. yakasance yana ba shi matsanancin kulawa fiye duk daukacin iyalin shi.


A shekara ta shida da haihuwarsa sai mahaifiyarsa ta tafi da shi ziyarar danginsa na nono, wato banu Udaiyyu bin najjar a Yathrib (Madina), a tare da su akwai Ummu Aiman Sai suka saura a can har na tsawon wata daya, sannan sai suka juyo suka kama hanyar dawowa Makka. A hanya ne ajali ya samu mahaifyarsa Amina, aka bisne ta a Abwa, wanda wani gari ne da ke tsakanin Makka da Yathrib (Madina).


Sai Ummu Aiman ta dawo da shi wajen kakansa, yayin da ita kuma ta dauki nauyin aikin uwa, kamar yadda kakansa Abdul-Mudallibi ya dauki aikin uba. Wannan kulawa dai ba ta jima sosai ba don shi ma wannan kaka nasa Allah Ya dauki ransa a lokacin Mustafa na da shekaru takwas da haihuwa.


Daga nan sai kulawarsa ta koma hannun Baffansa Abu Dalib , wanda ya yi mu'amala da shi da kauna, sassauci da lura irin ta iyaye, ta yadda babu wani daga 'ya'yansa da yasami irin hakan. Ya kasance yana barci a shimfidar baffansa, yana zama gefen shi, yana cin abinci tare da shi, yana fita tare da shi duk lokacin da ya fita daga gidansa; da wasun wadannan na daga nau'o'in lura da so wadanda irin suke da wuyan samu.


Muhammad (s.a.w.a) ya kasance yana girma a hannun baffansa alhali daukakan halayensa na girma tare da shi, ta yadda har sai da ya kebantu da wasu siffofi na nagarta a tsakaninsa da mutanensa da suka hada da gaskiya, rikon amana, daidaito da halin girma; wadannan siffofi dai sun kebanta da shi ne ban da waninsa; har ma ta kai ma mutanen suna kiransa da "Mai Gaskiya da Rikon Amana".


Ganin cewa dai ya fara girma kuma don kada ya zauna haka, Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) ya fara aiki a lokacin yana matashi. Aikin da ya fara yi shi ne kiwon tumaki/awaki. Sannan sai ya bi Baffansa Abu Dalib zuwa Sham don kasuwanci. 


A wannan lokaci ma dai Manzon Allah (s) ya nuna fasaha, kwazo, gaskiya da kuma rikon amana a wannan fage lamarin da ya jawo hankalin wata hamshakiyyar attijira mai suna Khadijah bint Khuwailid zuwa gare shi. Don haka sai ta nemi shi da ya kula mata da wani sashi na kasuwancinta, ta ba wasu dukiya mai yawan gaske don gudanar da kasuwanci, wanda daga karshe ta samu riba mai girman gaske da ba ta taba samu ba.

Baban humaid Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post