IRAN TA MAYAR DA MARTANI GA KASASHEN TURAI UKU AKAN CIGABA DA KAKABA MATA TAKUNKUMI.


 IRAN TA MAYAR DA MARTANI GA KASASHEN TURAI UKU AKAN CIGABA DA KAKABA MATA TAKUNKUMI.

Daga Bin Muhammad

Iran ta yi tir da matakin da kasashen Birtaniya, Faransa da Jamus su ka dauka na cigaba da kakaba ma ta takunkumi wanda a karkashin yarjejeniyar Nukiliya ta 2015 ya kamata ya zo karshe nan da wata daya.A jiya Alhamis ne dai kasashen na Birtaniya, Faransa da Jamus su ka jaddada cigaba da aiki da takunkumin da su ka kakaba wa jamhuriyar Musulunci ta Iran akan shirinta na Fasahar Nukiliya na zaman lafiya.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana matakin na kasashen uku da cewa; haramtacce ne, kuma ba ya kan doka, domin yana cin karo da yadda kasashen uku su ka amince da yarjejeniyar Nukiliya da kuma kudurin MDD mai lamba 2231 wanda ya amince da waccan yarjejeniyar.Dalilan da kasashen uku na turai su ka fake da shi wajen kakaba wannan takunkumin su ne cewa Iran din tana bai wa Rasha jiragen sama marasa matuki, sannan kuma za ta iya bai wa Moscow makamai masu linzami a yakin da take yi da Ukiraniya.

Iran dai ta sha yin watsi da wadannan zarge-zargen.
Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post