Wafatin Manzon Allah (S): MUSULMI NA DA ZABI GUDA BIYUMa'asumah Nigerian News Update


Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

Da sunan Ubangijin da ya yi ma AnnabinSa (S) shaida a cikin Alkur’ani mai tsarki da cewa: “Kuma (Muhammad (S) baya furuci bisa son ransa, face (duk abin da ya fada) wahayi ne aka yi a gare shi.” Allah (T) da yake wasiyya ga Muminai a cikin Alkur’ani da cewa: “Abin da Manzo (S) ya zo muku da shi ku rike shi, kuma abin da ya haneku a kansa ku hanu.”

Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta (S) wanda Allah ya yabe shi a cikin littafinsa mai tsarki, yana mai cewa: “Kuma lallai Kai (Annabi) kana bisa dabi'u masu girma.” Kuma ya yi masa garkuwa daga masu jingina masa gushewar hankali, a yayin da yake cewa: “Kuma sahibinku (Annabi (S) ba mahaukaci bane!”

A ranar 28 ga Safar, shekara ta 10 bayan hijira ne Manzon Allah (S) ya yi wafati. Ya koma zuwa ga Mahaliccinsa Madaukaki. Kafin wannan ranar abubuwa da dama sun faru, wanda mafi girmansu shine wanda ya auku a ranar Alhamis 24 ga Safar din.

Ranar 24 ga watan Safar, rana ce da tarihin Musulunci ba zai taba mancewa da ita ba, ba kuma zai kyale ta rika zuwa tana wucewa ba tare da raya musiba da ambaton bala’in da ta kunsa ba. Domin kuwa a irin wannan ranar ne na 24 ga Safar, aka shiga tsakanin Annabi (S) da wanzarwa al’ummarsa dauwamammiyar shiriya. A wannan ranar ne aka tabbatarwa da Manzon Allah (S) cewa ba za a taba bari shiriyar da ya zo da ita ta wanzu a kan gaba dayan al’ummarsa ba, sai ga ‘yan kadan daga cikinsu, wanda muna fatan Allah ya sa muna cikin kadan masu riko da shiriyar nan.

Ya zo a cikin littafin Sahihul Bukhari, Hadisi na 4431 da na 4432, daga Abdullahi Ibn Abbas (RA), yace: “Ranar Alhamis! Ko ka san abin da ya faru a ranar Alhamis din? Yace: Itace ranar da rashin lafiyar Annabi (S) ta tsananta. Sai Annabi (S) yace: “Ku kawo min abin rubutu na rubuta muku rubutun da ba za ku taba bata a bayansa ba har abada.” Sai suka yi jayayya, kuma bai cancanta su yi jayayya a gaban Annabi (S) ba! Sai suka ce; “Me ya dameku da shi? Ya fita hayyacinsa!” Inna lillahi wa inna ilaihi Raji’un!....1 Zamu Cigaba insha allah

                 Saifullahi m.kabir
          Baban Humaid' Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post