JANAZAR ANNABI .SAWW. AKAN ME SUKAYI JAYAYYA..? To, su waye suka yi jayayyar? A kan me suka yi jayayya? Kuma da wa suka yi jayayya din? Ibn Abbas ya bamu amsar a Hadisi na 5669, a cikin Sahihul Bukhari.


Hadisi na 5669, Hadisin Ibrahim bin Musa da Isinadinsa na mutane 7 wanda ya tuke izuwa ga Abdullahi Dan Abbas (RA), yace: “Yayin da ajali ya fuskato Manzon Allah (S), a dakin akwai mazaje (Sahabbai), daga cikinsu akwai Umar dan Khaddabi, sai Manzon Allah (S) yace; ‘Ku kusantoni (da abin rubutu) na rubuta muku rubutu wanda ba za ku bace ba a bayansa.’ Sai Umar yace: ‘Lallai rashin lafiya ya galabaitar da Annabi, kuma a wajenku akwai Alkur’ani, Littafin Allah ya wadatar da mu!’

Ibn Abbas yace: (Da Umar ya fadi hakan), Sai mutanen da ke cikin dakin suka samu sabani, (suka rabu gida biyu), suna masu husuma da junansu. Daga cikinsu akwai masu cewa; ‘Ku kawo wa Manzon Allah (S) ya rubuta muku abin da ba za ku bace ba a bayansa.’ Daga cikinsu kuma akwai masu cewa abin da Umar yace. (Wato kar a bayar, zafin ciwo ne ke damun Manzon Allah (S)). Yayin da wargi da sabaninsu ya yawaita a gaban Manzon Allah (S), sai Annabi (S) yace dasu; ‘Ku tashi daga gareni!”

A Hadisin aka karkare da cewa, Ubaidullahi yace; Ibn Abbas (RA) ya kasance yana cewa “Mafi girman dukkan abin bakin ciki shine abin da ya katange tsakanin Manzon Allah (S) da ya rubuta musu wannan rubutun, saboda sabaninsu da kuma warginsu.”

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post