SHIN MANZON ALLAH (s) YA FADI WASIYYAR DA ZAI RUBUTA MANA AKA HANA SHI?



 Ma'asumah Nigerian News Update

Eh ya fada. Kamar yadda aka kawo a cikin Sahihul Bukhari, hadisi na 4431 cewa ya yi wasicci da abubuwa guda uku, amma an mance na uku din. Gakiyar magana wasiyyar Manzon Allah (S) ta uku da ruwayar Bukhari yace an manta, Imamu Muslim ya kawo ta a cikin Sahihinsa, hadisi na 6378; A cikin wata huduba mai tsawo, Manzon Allah (S) yana cewa:

“Yaku Mutane, ku saurara. Ni mutum ne, kuma dan sakon Ubangijina ya kusa ya zo, zan kuma amsa masa. Ni na bari a cikinku nauyaya guda biyu; Na farkonsu shine Alkur’ani, wanda a cikinsa akwai shiriya da haske. Ku yi riko da littafin Allah ku bi shi; Da kuma Ahlulbaiti na. Ina gama ku da Allah akan Ahlulbait dina! Ina gama ku da Allah akan Ahlulbait dina. Ina hada ku da Allah akan Ahlulbait dina.”

Wadannan Ahlulbait din na Manzon Allah (S) da ya gwama mana wajibcin binsu da bin Alkur’ani, sune wadannan shugabanni 12 da Manzon Allah (S) ya fada mana su a cikin Sahihul Bukhari, hadisi na 7222 da na 7223, daga Jabir Dan Samura, yace; Na ji Annabi (S) yana cewa: “Shugabanni goma sha biyu za su kasance.” Sai ya fadi wata kalma da ban ji me yace ba. Sai babana yace, Annabi (S) yace ne; “Dukkansu daga Kuraishu suke.”

Ya hau kanmu mu tashi mu yi karatu tare da zurfafa bincike akan addinin nan. Mu san wadanda Manzon Allah (S) ya koma ga Allah (T) ya barsu a matsayin ababen riko masu koya mana addini. Mu kuma bi koyarwarsu wacce ita ce hakikar koyarwar Manzon (S). Allah ya tabbatar da mu akan shiriya.

- Saifullahi M. Kabir
Baban Humaid Mnnu//Ng0027
26 Safar, 1444 (23/09/2022)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post