AUREN MANZON ALLAH (S A W W) DA SAYYIDA DAHIRA AS.



Ma'asumah Nigerian News Update

A lokacin da ya cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa sai ya tafi kasar Sham don gudanar da kasuwanci da wannan dukiya da Khadija bint Khuwailid (r.a) ta ba shi, inda kamar yadda muka bayyana a baya aka riba mai girman gaske da ba a taba samun irintaba, hakan kuwa saboda albarkar da ke tattare da Annabin ne da kuma irin gaskiya da rikon amanarsa wadannan abubuwa dai sun faranta wa Khadijah rai kwarai da gaske da kuma kaunar Annabin.


Khadija dai ta kasance daga zababbun matan Kuraishawa kuma ta fi su kudi da kyau iatadai sayyida Khadija as an haifetane a garin Makka kuma a can ta girma, tun a lokacin jahiliyya ana kiranta da tahira" (tsarkakakkiya), saboda irin kyawawan halaye da take da su a tsakankanin matayen Kuraishawa.


A lokacin da ta ba wa Manzon Allah (s) dukiyarta don kula mata da su wajen kasuwanci, Khadijah ta hada shi da wani amintaccen yaronta mai suna Maisara. Irin kyawawan halayen Manzon Allah (s.a.w.a) dai sun yi tasiri wa maisara, don haka sai ya tafi wajen Khadija yana gaya mata irin dabi'un Muhammad (s.a.w.a) da ya gani, 


Hakan yasa son Manzo ya shiga zuciyarta, sai ta bukace shi da ya aureta, ya zama mijinta, alhali kuwa ta ki amincewa da manyan Kuraishawa wadanda suka zo neman auren nata. 


Manzo(s.a.w.w) dai ya amince da wannan bukata ta Khadijah, inda ya aureta, inda suka tabbatar da mafi kyaun kusanci da ake iya mafarki, wanda ya kyautatu da kauna,alkawari da tausayin juna, suka shata mafi kyawun sura na rayuwar auratayya mai nasara.

Baban humaid Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post