Yadda HUKUMAR Leken asiri ta Iran ta cafke Mr. Frank Genin tare da wasu abokan aikinsa yan MOSSAD.


 Nasir Isa Ali 


Yadda aka cafke Mr. Frank Genin tare da wasu abokan aikinsa yan MOSSAD.


HUKUMAR Leken asiri ta Iran ta fitar da wasu takaitattun bayanai game da yadda ta cafke wasu yan MOSSAD a cikin kasarta. Kamar yadda aka sani ne, yadda Iran ke samun cigaba a fannin kere kere musanman ta bangaren tsaro, wannan lamarin yana damun kasashen yammacin duniya. Don haka cikin yakin da suke yi da Iran shine na kokarin gano masana, musanman bangaren fasaha da kimiyya domin kashe su.Hanyoyin da makiya suke bi domin gano masanar suna da yawan gaske, wannan ne yasa ita ma Iran ta tashi tsaye domin gano masu yunkurin gano masanan nata domin katse musu hanzari. Wannan labarin da MOIS ta fitar yana daga cikin hanyoyin da makiya suke bi domin gano masanar Iran din.

Israila tayi hayar wani bayahude wanda ya bayyana kansa a matsayin dan kasar Sweden, mai suna Frank Genin, inda ya rubutawa kamfanonin kere kere na kasar Iran wasika inda yake gayyatarsu zuwa taron bita da baje kolin kayayyaki, wanda kamfaninsa zasu yi a kasar Malaysia. Kanfanonin Iran din da Mr. Frank ya rubutawa wasikar duk cikarsu MOSSAD na zargin suna da alaka da bangaren kere kere na ma'aikatar tsaron Iran. Babban aikin wannan masanin tattara bayanan (Mr. Franka) shine ya gano shugabannin kamfanonin, sannan ya tattara bayanan sirri masu inganci a kansu. Mr. Genin ya bayyana musu a cikin wasikarsa cewar kamfaninsa na kera kayan sifefas (Spare Parts) kuma galibin kayan sun san cewar Iran na da bikatarsu.Kamfanonin Iran din, bayan sun yi nazarin wasikun da Mr.Genin ya aiko musu sai suka bada amsa cewar sun amsa gayyatar tasa. Abin ka da "kifi na kallonka mai jar koma' sai ya gayyaci iraniyawan zuwa kasar Malaysia, isarsu can ke da wuya sai Mr. Genin ya mikasu ga wani dan MOSSAD din mai suna Mr.Hadrien Lavaux domin dorawa daga inda shi Mr.Genin ya tsaya.

Mr. Genin ya bayyana wa iraniyawan cewar Shi Mr. Hadrien shine babban MD na kamfanin "Triple A Industries" an Aerospace advanced alloys and composites company" kuma an kirkiri kamfanin ne a kasar Singapore a shekara ta 2017 kuma yana da abokan hurda a kasashe da dama a duniya.

Daga lokacin sai su yan MOSSAD din suka samu ittisali da wasu daga cikin daraktocin kamfanonin iran masu kere kere da kuma aiki a ma'aikatar tsaron Iran din. Kuma lokaci bayan lokaci suna gayyatar iraniyawan zuwa taron bita domin samun damar tatsar bayanai daga garesu. Wannan kuma ya baiwa su yan Mossad din damar gano abubuwan da ma'aikatar tsaron Iran din ke bukata domin aikinsu. Sannan sun gano masu jagorantar ma'aikatar tsaro da kuma masu yi musu kasuwanci da nemo musu kayayyakin bukatuwarsu na yau da kullum. Wannan ne yasa su yan MOSSAD din suka sake gayyatar wasu masana dag Iran din zuwa taron bita da musanyen bayanai a kasar Turkiye da Hungary da Oman da kuma kasar Georgia, wannan karon sai aka sirranta tafiye tafiyen nasu domin bai wa su yan Mossad din damar bayyanawa wasu iraniyawan burinsu da kuma abin da suke nema su gano Abinka da wanda ya fika wayo, su kuma yan Mossad basu san cewar Rabin abokan hurdar nasu duk ma'aikatan MOIS bane, kuma basu san cewar duk takun da suke yi suna yinsa ne a kan tafin hannun hukumar leken asirin Iran bane.

A karshe dai wadannan yan Mossad din duk sun fada hannun MOIS.

WANNAN rahoton ministan leken asirin Iran Hujjatul Islam khatib ne ya fitar dashi ya karanata sannan ya rabawa yan jarida.

Nasir Abu Muhammad

Real Naseer Umar 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post